ASUU: Yajin aiki ba shi ne kaɗai mafita ba

Matakin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yanke na tsawaita yajin aikin da ta fara har na tsawon makonni takwas, ya dagula wa ɗalibai, iyaye da kuma masu ruwa da tsaki a harkar ilimi lissafi, domin yajin aikin zai ƙara dagula al’amuran ilimi a jami’o’in ƙasar nan.

Da ya ke yin biris da yadda harkar ilimi da tarbiyya ke durƙushewa a sanadin yajin aikin malaman jami’o’i, shugaban ASUU na yanzu, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya bayyana yajin aikin na watanni biyu a makon da ya gabata, ya bayar da hujjar cewa, “bayan ɗaukar rahotanni kan ayyukan da manyan jami’an gwamnati su ka yi, ƙungiyar ta kammala da cewa gwamnati ta gaza wajen gamsar da duk wasu batutuwan da aka taɓo a cikin yarjejeniyar da ƙungiyar ASUU ta yi a shekarar 2020 a cikin yajin aikin na tsawon makonni huɗu, inda ta yanke shawarar shiga wani yajin aikin na wasu makonni takwas don bai wa gwamnati ƙarin lokaci don magance dukan matsalolin ta yadda ɗalibansu za su dawo makarantunsu.”

Tun a shekarar 2009 da gwamnatin tarayya da ASUU suka sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2001, ASUU ta yi yajin aiki har sau takwas, na tsawon wata ɗaya, wasu kuma har na tsawon watanni biyar, amma duk da haka gwamnatin ba ta biya masu buqatarsu tare da cike sharuɗɗan yarjejeniyar ba. Mafi muni kuma, babu ɗaya daga cikin manufofin yarjejeniyar huɗu da aka cimmawa duk da yajin aikin da ake yi.

Muhimmancin sake sasantawa na 2009 ya haɗa da; 

  1. Don kawar da matsalolin da ke cikin Tsarin Jami’o’i, don mayar da su kan hanyar da ta dace don cigaban ƙasa.
  2. Don samar da walwalar ma’aikata, ba kawai ta hanyar haɓaka albashin ma’aikatan ilimi ba, har ma ta hanyar kawar da su daga cikin abubuwan da ke tattare da tsarin biyan albashi na ma’aikata.
  3. Don dawo da jami’o’in Nijeriya kan hanya da gaggawa, da tsayawa tsayin daka wajen samar da ingantaccen ilimi.
  4. Don tabbatar da ’yancin cin gashin kai na jami’o’i’ da ’yancin ilimi.

Duk waɗannan an yi su ne don nuna yadda yarjejeniyar ta 2009 ta zo daidai da burin malaman jami’o’in, takardar mai shafi 51 ta ƙunshi ƙudirori biyar na gyara dokokin da suka shafi fannin ilimi.

Sama da yajin aikin takwas tun daga waccan yarjejeniya, duk ba a samu nasara ba, ya kamata ASUU ta gane cewa yajin aikin ba zai zama hanya ɗaya tilo da za a bi ba, don haka ya kamata a ce ta ɓullo da wasu hanyoyi na shawo kan gwamnati ta cika alƙawuran da ta ɗauka. Ta hanyar yajin aiki akai-akai, martabar ASUU ya ci gaba da taɓarɓarewa, ɗalibai suna takaici, darajar karatun manyan jami’o’i na ci gaba da faɗuwa, yayin da darajar digirin da jami’o’inmu ke bayarwa ke raguwa. Domin kaucewa waɗannan manyan matsaloli da dama, ASUU ta sake tunani wajen tattaunawa da matsa wa gwamnati kan ta cika alƙawuran da ta ɗauka.

Don haka, Blueprint Manhaja na kira ga ƙungiyar ASUU da ta janye yajin aikin da ta ke yi domin biyan buƙatun ɗalibai tare da yin amfani da wasu hanyoyi wajen tursasa gwamnati. Na farko yana da kyau a matsa wa gwamnati don komawa kan tattaunawa da sabbin tawaga na shugabannin da ministan ilimi Malam Adamu Adamu ya kafa. Baya ga wannan sabuwar tawaga ta tattaunawa, ASUU za ta kuma iya neman goyon bayan ’yan majalisar dokokin ƙasar wajen matsa wa gida hujjarta na inganta tsarin jin daɗin jama’a da samar da kuɗaɗen shiga na jami’o’i. Idan aka yi aiki mai kyau kuma na gaske, Majalisar za ta iya tabbatar da cewa an yi gyara ko kuma a saka kasafin kuɗin ilimi na shekara don yin la’akari da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da ASUU.

Wata hanyar da ke ƙara matsa lamba ga gwamnati ita ce zanga-zangar da malamai da ɗalibai ke yi akai-akai domin jawo hankalin kowa da kowa kan gazawar gwamnati wajen kiyaye sharuɗɗan yarjejeniyoyin da aka ƙulla. Yana da kyau a ci gaba da jan hankalin gwamnati a kan hanyar da za a bi fiye da yajin aikin da ke zubar da kimar ƙungiyar ASUU da jefa ɗalibai cikin qunci.

Haka kuma, ASUU dole ne ta leka ciki yayin da ta ke lalubo hanyoyin magance ƙalubalen da ke fuskantar ilimin jami’o’i a Nijeriya. Sanin kowa ne cewa masu gudanar da jami’o’in ba su da gaskiya ga kuma riƙon sakainar kashi wajen tafiyar da kuɗaɗen shiga da ake samu a cikin gida. Masu kula da manyan makarantu na sace kuɗaɗen da ya kamata a yi amfani da su wajen inganta ababen more rayuwa a ƙarƙashin hancin malamai ta hanyar rashin gudanar da ayyukansu da kuma ƙaran kwangila.

Misali; a watan Nuwambar 2019, Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da sauran Laifuka (ICPC), ya bayyana a yayin taron ƙasa kan rage cin hanci da rashawa a ɓangaren gwamnati cewa, binciken da ICPC ta gudanar ya nuna cewa jami’o’i na daga cikin waɗanda suka fi fuskantar matsalar cin hanci da rashawa. Hukumar ta ICPC ta bayyana sunayen jami’o’i da asibitocin jami’o’i da dama da aka gano sun yi qarin kasafin kuɗin ma’aikatansu har na ɗaruruwan miliyoyin naira.

Dole ne malamai su ƙalubalanci irin wannan gurɓataccen tsari a matsayin hanyar tabbatar da amfani da IGR a cikin jami’o’inmu. Muna goyon bayan matakai daban-daban da yawa don magance matsalolin da ke fuskantar manyan jami’o’i a Nijeriya, amma mu na adawa da yajin aiki, wanda ke lalata ɗalibai da sauran al’umma.