Atiku da Obi sun yi ganawar farko tun bayan shan kaye a zaɓen 2023

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da takwaransa na Jam’iyyar Labour, Peter Obi, sun yi ganawa domin tattauna gwagwarmayar siyasarsu.

Wannan dai shi ne karon farko da aka ga ƙusoshin siyasar sun gana tun bayan da suka sha kaye a hannun Bola Tinubu a babban zaɓen 2023.

Atiku da ne ya tabbatar da ganawar tasu a shfinsa na X a ranar Litinin.

Ganawar tasu ba ta rasa nasaba da neman haɗewa a don kafa jam’iyya wadda za su yaƙi Tinubu da ita a 2027.

Idan ba a manta ba, kwanakin baya aka jiwo masanin tattalin arzikin nan, Pat Utomi, a cikin wata hira da tashar Channels TV ta yi da shi yana cewa, ‘yan takarar shugabancin ƙasa uku a babban zaɓen da ya gabata, wato Atiku Abubakar da Peter Obi da kuma Rabiu Kwankwaso sun amince su kafa jam’iyya don yaƙar jam’iyya mai mulki ta APC a 2027.