Atiku ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe

Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar PDP a babban zaɓen 2023, Abubakar Atiku, ya garzaya Kotun Ƙoli don kotun ta yi watsi da hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke a ranar 6 ga Satumba.

A hukuncin da ta yanke, Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen ta ce Bola Ahmed Tinubu shi ne wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a babban zaɓen da ya gabata.

Sai dai, Atiku ya ce kotun ta tafka kuskure a hukuncin da ta yanke ranar Talata ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Simon Tsammani.

Ƙarar da Atiku ya ɗaukaka ta hannun babban lauyansa, Chief Chris Uche, SAN na neman Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta yi watsi da dukkan bincike da hukuncin da kotun farko ta yi bisa dalilin cewa ba su yi daidai da ƙarar da ya shigar ba.

Daga cikin dalilan da suka sanya Atiku ɗaukaka ƙarar har da batun cewa, Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen ta yi wa doka karan tsaye na ƙin soke zaɓen Shugaban ƙasar da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun 2023.

Atiku ya ce ba a bi Dokar Zaɓe ta 2022 sau da ƙafa ba a yayin zaɓen.