
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya caccaki rahotannin da ke cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da mayar da kuɗin jarabawar WAEC da NECO zuwa N50,000 ga kowane ɗalibi daga shekarar 2027.
A sanarwar da Kakakinsa, Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya ce wannan mataki tare da ƙarin kuɗin makarantun Unity Colleges zai ƙara jefa iyaye cikin wahala tare da hana miliyoyin yara samun ilimi.
Ya bayyana cewa, Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke da mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, yana mai cewa ƙara kuɗin jarabawa zai ƙara yawan yaran da za su rasa damar cigaba da karatu, musamman daga iyalai marasa ƙarfi.
Akan haka ne ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya janye shirin ƙara kuɗin jarrabawar tare da rage kuɗin makarantun gwamnati.
Haka kuma, ya kirayi gwamnati da ta ƙara zuba jari a fannin ilimi, faɗaɗa cibiyoyin ilimi da kuma tabbatar da cewa talauci bai hana kowane yaro samun ilimi ba a Nijeriya.
