Daga USMAN KAROFI
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya karɓi bakuncin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, a gidansa da ke Jihar Adamawa.
Atiku ya bayyana wannan a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin X a ranar Asabar.
A rubutun da ya yi, ya ce: “Lokacin karin kumallo tare da abokina, Peter Obi.’” A bidiyon, an ga manyan shugabannin biyu, tare da wasu mutane, zaune a kan tebur suna shirin cin abinci.
Wannan ba shi ne karo na farko da suka haɗu bayan zaɓen 2023 ba, domin sun gana a baya a watan Mayu na wannan shekara. Obi ya kuma kai ziyarar ban girma ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a gidajensu da ke Abuja a watan Mayu. Wannan ziyara ta Obi ta zo ne bayan ya bar PDP ya koma LP a watan Mayu 2022. A wancan lokaci, babban mai magana da yawun kamfen ɗinsa, Yunusa Tanko, ya bayyana cewa tattaunawar da suka yi da manyan jiga-jigan PDP ta ta’allaƙa ne kan yadda za su ceto Nijeriya daga mulkin jam’iyyar APC mai ci.