Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala a ƙaramar hukumar Gwamna Wike ta Okrika ta jihar Ribas.
Okrika ta kasance hedikwatar ƙaramar hukumar mahaifar uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Dame Patience Jonathan ce, da kuma babban darakta na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a jihar Ribas, Dakta Abiye Sekibo.
Atiku ya samu ƙuri’u 8,476 inda ya doke ’yan takarar jam’iyyar LP da APC, Peter Obi da Sanata Bola Ahmed Tinubu, wanda suka samu ƙuri’u 4,018 da ƙuri’u 2,729.