Atiku ya lashe Gombe a dukkan ƙananan hukumomi 11

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lashe dukkan ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe.

A sakamakon zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana a safiyar ranar Litinin, jami’ar da ke kula da zaɓen, Farfesa Maimuna Waziri, mataimakiyar shugabar jami’ar tarayya ta Gashua, ta ce Atiku ya samu ƙuri’u 319,123 kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya samu ƙuri’u 146,977.

A sakamakon da aka bayyana daga ƙaramar hukumar Shongom, Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u 13,520 yayin da APC ta samu 7,525; Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu ƙuri’u 2,579 yayin da Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP ya samu ƙuri’u 256.

A ƙaramar hukumar Balanga Atiku ya samu ƙuri’u 23,326, Tinubu 11,715, Obi ya samu 3,760, Kwankwaso ya samu ƙuri’u 405.

A ƙaramar hukumar Nafada, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ya samu ƙuri’u 12,339 yayin da APC ta samu 8,242, NNPP ta samu ƙuri’u 344 yayin da Labour Party ta samu ƙuri’u bakwai kawai.

A sakamakon bayyana sakamakon ƙaramar hukumar Funakaye, PDP ta samu ƙuri’u 25,384, APC ta samu ƙuri’u 12,672, NNPP ta samu ƙuri’u 767, jam’iyyar Labour ta samu ƙuri’u 320.

A karamar hukumar Yamaltu/Deba, PDP ta samu ƙuri’u 38,479 yayin da APC ta samu 18,896, NNPP ta samu 1,591 yayin da Labour Party ta samu 740. A ƙaramar hukumar Kwami, PDP ta samu 24,068, APC ta samu 16,245, NNPP 820, yayin da Labour Party ta samu 78.

A ƙaramar hukumar Billiri, PDP ta samu 21,991 yayin da APC ta samu 7,232, yayin da Labour Party ta samu ƙuri’u 8,898, NNPP kuma ta samu 653. A ƙaramar hukumar Dukku, PDP ta samu ƙuri’u 21,579 yayin da APC ta samu 12,925. Yayin da jam’iyyar NNPP ta samu ƙuri’u 899 yayin da jam’iyyar Labour ta samu ƙuri’u 49.

A ƙaramar hukumar Akko, PDP ta samu ƙuri’u 55,202 yayin da APC ta samu ƙuri’u 22,749. Jam’iyyar Labour ta samu ƙuri’u 2,241 yayin da NNPP ta samu 1,284. A ƙaramar hukumar Kaltungo, PDP ta samu ƙuri’u 20,968, APC 2,464, yayin da jam’iyyar Labour ta samu ƙuri’u 5,149, yayin da NNPP ta samu ƙuri’u 486.

A ƙaramar hukumar Gombe, wadda ita ce ta ƙarshe da aka ayyana, PDP ta samu ƙuri’u 62,347 yayin da APC ta samu ƙuri’u 19,312. Jam’iyyar NNPP da Labour ta samu ƙuri’u 3,015 da ƙuri’u 2,389.