Atiku ya lashe mazaɓu 9 daga cikin 10 a Kebbi ta Tsakiya

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe ƙananan hukumomi 9 cikin 10 da aka kammala ƙirgawa inda ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar, APC Bola Ahmed Tinubu, ya lashe ƙaramar hukuma ɗaya.

An kusa kammala kidayar kuri’un dan takarar Sanata na Kebbi ta tsakiya. Yanzu haka an tattara sakamakon ƙuri’u na ƙananan hukumomin Gwandu, Aliero, Kalgo, Bunza, Koko Besse, Maiyama, da Jega.

Sai dai har yanzu ana jiran sakamakon ƙaramar hukumar Birnin kebbi. Rahotanni na cewa an sami hakan ne sakamakon batan dabon Jami’in tattara sakamakon zaɓe na gundumar Marafa da ke karamar hukumar Birnin kebbi. Tare da sakamakon zaɓe na gunduma ta Marafa.

Kamar yadda wakilinmu ya kalato, ɗan takarar Sanata na Kebbi ta tsakiya a jam’iyyar PDP, Sanata Adamu Aliero, ya sami nassarar lashe zaɓen ƙananan hukumomi 7 da aka kammala sakamakon zaɓen nasu.

Dan takarar Majalisar wakilai na jam’iyar PDP Ibrahim Haliru Muhammad ya lashe sakamakon zaɓe na kananan hukumomi uku da suka haɗa da Birnin Kebbi da kalgo da Bunza da aka kammala ƙirgawa, Kowane lokacin daga yanzu ana idan an kammala tattara sakamakon zaben mazaɓar za a sanar.