Atiku ya naɗa Dino Melaye da Daniel Bwala a matsayin kakakinsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, Atiku Abubakar ya naɗa Sanata Dino Melaye da Dakta Daniel Bwala a matsayin masu magana da yawun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a yaƙin neman zaven shugaban ƙasa mai zuwa.

A cewar sanarwar da mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya sanyawa hannu, naɗin na biyu ya fara aiki nan take.

Malaye ɗan siyasa ne kuma ɗan majalisar dattawa ta 8, wanda ke wakiltar mazaɓar Kogi ta Yamma. Ya fito daga Ayetoro Gbede da ke ƙaramar hukumar Ijumu a Jihar Kogi

Bwala, a ɗaya ɓangaren, ƙwararre ne a fannin shari’a, ɗan siyasa kuma manazarci harkokin jama’a. Ya fito daga Jihar Borno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *