Atiku ya roƙi gwamnati kada ta dakatar da hada-hadar kuɗaɗen intanet

Daga FATUHU MUSTAPHA

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya roƙi gwamnatin Shugaba Buhari kada ta dakatar da hada-hadar kuɗaɗen intanet wanda aka fi sani da ‘cryptocurrency’ a Turance.

A Juma’ar da ta gabata Babban Bankin Nijeriya (CBN) aya bada umarnin bankuna da dangoginsu su rufe duka asusun da ke da alaƙa da harkar kuɗaɗen intanet ba tare da ɓata lokaci ba.

A wata sanarwa da ya sanya wa hannu Asabar da ta gabata, Atiku ya ce kamata ya yi gwamnati ta ɗauki matakin sanya wa harakar ido maimakon daƙile ta baki ɗaya.

Tare da bada misalin yadda hada-hadar kuɗaɗen ƙetare a Nijeriya ta yi ƙasa daga Dalar Amurka bilyan 23.9 a 2019 zuwa Dala 9.6 a 2020, yana mai cewa tattalin arzikin ƙasa na buƙatar a faɗaɗa shi ne maimakon takurewa.

“Muna da buƙatar buɗa wa tattalin arziƙinmu maimakon rufewa.

“Babbar ƙalubalen da ke fuskantar Nijeriya shi ne rashin aikin yi ga matasa. Gaskiyar ita ce, abin ya wuci gaban ƙalubale sai dai yanayi mai buƙatar kulawa cikin gaugawa. Hakan na takura wa tattalin arzikinmu da kuma haifar da cikas ga tsaron ƙasa.”

Atiku ya ci gaba da cewa, “Abin da Nijeriya ta fi buƙata a halin yanzu shi ne samar da ayyuka da kuma buɗa wa tattalin arzikinmu. Da ma dai ƙasar na fama da matsalar tattalin arziki sakamakon rufe iyakokin ƙasa a dalilin ɓullar annobar korona.

“Wannan ba shi ne lokacin da ya dace a sanya wata doka da za ta hana shigar kuɗaɗe Nijeriya ba. Sannan ina kira da a sake duba batun haramta mu’amala da kuɗaɗen intanet da aka yi.”

A cewarsa, “Wajibi ne mu samar da ayyuka a Nijeriya. Tilas ne a gare mu mu faɗaɗa tattalin arzikinmu. Ya zama dole mu kawar da duk wani abu da zai yi wa sha’anin zuba jari tarnaƙi. Akwai haƙƙoƙi da dama na ‘yan Nijeriya a kanmu waɗanda akwai buƙatar mu sauke su.”