Atiku ya yi gargaɗi kan hukuncin kotu da ya hana a ba Jihar Ribas kuɗaɗenta daga CBN

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi gargaɗi ga ɓangaren shari’a game da yadda za ta sa Jihar Ribas cikin rikici sakamakon hukuncin da kotun tarayya ta yanke a Abuja ranar Laraba, inda ta umarci bankin CBN da ya dakatar da biyan kuɗi ga jihar.

A cikin wata sanarwa da mai bashi shawara kan harkokin watsa labarai, Paul Ibe ya fitar, tsohon mataimakin shugaban ya ce abin baƙin ciki ne yadda wasu masu biyayya ga gwamnatin tarayya ke jan lamarin. Atiku ya yi mamaki yadda Alƙali Joyce Abdulmalik ta bayar da wannan hukunci yayin da kowa ya san Jihar Ribas ta riga ta kai ƙara kan hukuncin kotun game da kasafin kuɗin 2024.

Alƙalin ta hana bankin CBN, Aknta Janar na Tarayya, Bankin Zenith da kuma Access Bank daga ci gaba da baiwa Gwamna Fubara damar samun kuɗi daga asusun haɗin Kai na tarayya.

Atiku ya ce, kafin a bayar da hukuncin, babban lauya Femi Falana (SAN) ya riga ya sanar da babban alƙalin Kotun Tarayya, Alkali John Tsoho game da yiwuwar cin hanci bayan da aka ba wa alƙalai kyautuka a Abuja. Ya ce abin baƙin ciki ne ba a damu da gargaɗin Falana ba. Ya kuma ce jihar Ribas na samar da kashi 25 cikin 100 na man fetur na Nijeriya, don haka ya kamata Shugaba Tinubu ya ajiye tunanin zaɓen 2027 ya kula da amfanin Nijeriya.