Attajiri Otedola ya saka First Bank a aljihunsa

Daga AMINA YUSUF ALI

Yanzu haka, biloniyan ɗan kasuwar nan mai suna Femi Otedola shi ne mutum na farko daga cikin jerin masu hannun jari a bankin First Bank.

Biloniyan ya samu nasarar ɗarewa kan matsayin wanda ya fi kowa zuba hannun jari a bankin bayan ya sake sayen ƙarin kaso 2.5 na hannun jarin kamfanin FBNH wanda FBNH shi ne ubangidan bankin na First Bank.

Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu ma Otedola yana da hannun jari kaso 7.57 a FBNH. Abinda ya kai har ya doke Tunde Hassan-Odukale, Ciyaman ɗin FBNH a ƙarfin hannun jari a kamfanin. Kuma ya ba shi tazara mai nisa.

Saboda wannan matsayi nasa, a yanzu haka Otedola ya ƙara samun damar zaɓar wasu daraktocin kamar yadda da ma a baya ya taɓa samun damar haka. Inda ya zaɓo daraktoci biyu, ɗaya a First Bank, ɗaya kuma a HoldCo.

Idan za a iya tunawa, a cikin watan Octoba, 2021 da ya gabata ne, dai kamfanin Canji na Nijeriya (NGX) ya bayyana a tukararsa ta yanar gizo cewa, Hassan-Odukale shi ne mutumin da ya zama ma fi zuba jari mai tsoka a bankin.

Sai dai kuma wata guda kacal da waccan sanarwar sai aka samu labarin Otedola ya doke shi Hassan-Odukale a ƙarfin hannun jarin. Abinda ya cigaba da yaɗuwa a cikin kafafen yaɗa labarai.