Aubameyang ya buƙaci ninkin albashin Ibrahimovic a AC Milan

Ɗan wasan gaba na Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, yana neman sau biyu abin da Zlatan Ibrahimovic yake samu a AC Milan don komawa qungiyar ta qasar Italiya.

AC Milan ita ce kulob na baya-bayan nan da ake alaƙanta ta da ɗan wasan mai shekaru 32, wanda a yanzu ba a san makomar shi ba a Emirates.

Tun a ranar 6 ga watan Disamba, Aubameyang bai taka leda a Gunners ba, lokacin da Arsenal ta sha kashi da ci 2-1 a Goodison Park.

An cire ɗan wasan na Gabon ne daga muƙamin kyaftin ɗin ƙungiyar bayan mako guda bayan wani sabon ladabtarwa da ya aikata wanda kuma tun lokacin aka tilasta masa yin atisaye shi kaɗai.

Kocin Arsenal, Mikel Arteta, yanzu yana neman ɗauko Aubameyang.

AC Milan na sha’awar dawo da Aubameyang San Siro shekaru 11 bayan ya fara haskawa, inji Football Italia.

Tuni dai ƙungiyar Stefano Pioli tana da Olivier Giroud da Zlatan Ibrahimovic amma dukkansu sun yi fama da rauni a wannan kakar.