Auren cin zarafi: Anya haƙuri ne kawai mafita?

Daga AMINA YUSUF ALI

Sannun ku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Yau ma ga mu a wani makon mai albarka. A wannan makon muna tafe ne da bayani a kan yadda matan auren da suke fuskantar cin zarafi a gidan aure musamman a ƙasar Hausa. Inda za ka ga cewa, mace ana cin zarafinta, ana hana ta abinci, da sauran haƙƙoƙinta na aure ga uwa uba kuma duka da wulaƙanci. Amma ta kafe ta haƙura ta zauna a gidan. Me yake kawo hakan? Kuma anya haƙurin shi ne mafita? Idan ba shi ba ne mafita, to mecece sahihiyar mafitar? A sha karatu lafiya. 

Mai karatu in dai ya fito daga yankin ƙasar Hausa ba zai kasa sanin cewa cin zarafi da tauye haƙƙin mata da dukansu wata babbar matsala ce da ta addabi yankin ba. Kuma suna daga dalilan da sukan kawo yawaitar mace-macen aure. Idan kuma auren bai mutu ba a yi ta shan wuya iya wuya. Wani zubin mutane suna ganin baiken matar da take cikin irin wancan auren na cin zarafi. Suna ganin me zai hana ba za ta kama gabanta, sawunta a likkafa ba kawai ta wuce wajen? To babbar matsalar irin wannan auren ya fi komai wahalar bari. Ga shi tana shan wahalar. Ku da kuke gefe kuna tausaya mata, kuna jiye mata ciwon abin, ita kuma tana zaune da abinta. Ga wasu daga cikin dalilan da suke sa mata zama a gidan auren da ake cin zarafinsu ko ake tauye musu haƙƙinsu:

Dalili na farko shi ne, wasu matan ko da sun yi niyyar kama gabansu, sai mazan su hana su. A yi, a yi su rabu da su, su ƙi. Wani ma har danganawa da kotu ake yi amma ba zai saki ba. Sai dai a yi ta tafka shari’a. Ya gwammce ya bi dukkan wasu hanyoyi da matar ba za ta samu nasara ba. Kuma da ma mazan da ba a jin daɗinsu sun fi kowa ƙin yin saki. Wani har malamai zai shiga ya yi ta addu’a don ya samu ya kafe ta. Shi dai ta zauna ya cigaba da muzguna mata. Abinda bai gane ba, da a ce dukiya da ƙarfin da yake amfani da su, da zai juya su izuwa kyautata mata da wataƙila da ta so zama da shi ma tsakaninta da Allah. Mace fa idan ka kyautata mata ka gama da ita.

Na biyu, ‘ya’ya. Mun riga mun sani mata abinda suke fara sakowa a gaba kullum shi ne yaransu. Idan miji yana azabtar da mace, ko da ta yi niyyar guduwa don sama wa kanta lafiya, to ba ta iyawa saboda tunanin za ta bar su a cikin wahalar da ta guje wa kanta ɗin. Ko ma wasu wahalhalun da za su iya tasowa a gaba. Wata kuma tana tausaya musu kada su taso ba tare da uba ba, ko uwa. Ba sai na yi dogon bayani a kan matsalolin da ‘ya’yan da mace ke fuskanta a ƙasar Hausa ba. Da kuma ‘ya’yan da suka taso a hannun matar uba. 

Na uku, akwai matsala ta Iyayen matar ko wani nata mai faɗa a ji.   wasu iyayen su suke tilasta ta, ta koma duk lokacin da ta yi yunƙurin guje wa azabar da take ciki. Wasu iyayen har cewa suke idan ta fito ba su, ba ita. Ko kuma za su tsine mata idan ta fito. Shi ya sa sai ta zama ba ta da zaɓi sai dai ta zauna a cikin azababben auren. Ko da yana hana ta abinci, iyayenta sukan haɗa mata kayan abinci su sake tura ta ta koma. Kuma abin takaicin wani auren ma duk da hakan sai ya mutu. An gudu dai ba a tsira ba. Gara ma da kiransa aka yi, aka nusar da shi haƙƙin nasa.

Na huɗu, akwai al’ummar da muke ciki. Ita ma ta bayar da gudunmowa sosai. Kina fitowa daga aure, laifinki ne, mugun hali gare ki. Ba ma idan kin yi auren kin fito fiye da sau ɗaya. Al’ummarmu ta yi ƙaurin suna wajen tsangwamar bazawara. Kuma an riga an yarda da ma ba a auren daɗi wai dole aure zaman haƙuri ne. Ko ina aka samo wannan? Wannan zai sa ta yi ta tsoron fitowa don kada a kalle ta a mara haƙuri kuma mara kirki. 

Na biyar, akwai so. Hausawa sun ce, ‘so hana ganin laifi’. Tsakanin kuma mata da miji, sai Allah. Idan mace na son namiji duk irin cin zarafinta da zai ko ya tauye mata haƙƙi, tana iya shanyewa da kau da kai, tare da yi masa uzuri. Wata har ɗora ma kanta laifi take a zuciyarta don ta kare abin son nata. Wata ko ta fusata ta tafi ɗin, haka za ta haƙura ta sake dawowa wajen masoyin nata, shi kuma ya cigaba daga inda ya tsaya a cin zarafinta. Ba ma idan ya iya ba ta haƙuri da yin tausasan lafuzza ko ya iya yi mata wata kyauta a matsayin toshiyar baki. Duk lokacin da ya ɓata mata rai. Wata duk dukan da ya yi mata, in dai ya iya rarrashi, a take za ta yafe. 

Na shida, akwai igiyar zato.  Namiji yana azabtar da mace, amma kullum tana yi masa fatan zai gyara watarana. Wasu matan tsananin so ne yake rufe musu ido. Wasu kuma, huɗubar magabata ce.  Sai a ce, idan namiji yana cin zarafinki, to ki yi ta haƙuri watarana sai labari. Amma kafin ki ba da labarin fa? Allah ya sa ma azaba ba ta kashe ki ba, da za ki ba da labarin.

Na bakwai, jahilci da rashin sanin mutuncin kai. Kawai ita gani take ta cancanci wannan cin zarafi da ake yi mata. Sannan tana da ƙarancin ilimin gano haƙƙoƙinta. 

Na takwas, akwai Raunannen tunani. Mutumin da yake cin zarafin mutane da ma yana da wani babban makami, wato raunana tunanin wanda yake cutarwar. Ya mur]e zancen ya nuna shi wanda ake cutarwar shi ne mai laifin. Haka wannan tunanin zai ta wanzuwa a zuciyar mace ya hana ta taɓuka komai don fitar da kanta daga rayuwar cin zarafin. 

Na tara, akwai rashin rashin samun ƙwarin gwiwa. Mace idan tana cikin rayuwar azaba ta gidan miji, ko da ta farga ta gano cewa, ta gudu kawai shi ne mafita, amma abin fa ba mai sauƙi ba ne. Sai ta yi ta sa rana. Daga ƙarshe mata da dama ba sa cin nasara. Ƙalilan Allah yake taimaka su iya cimma burinsu. 

Na goma, sabo. Hausawa sun ce, sabo turken wawa. Mata da yawa suna kasa guduwa su bar gidajen auren da ake cuzguna musu saboda sabon da suka yi da gidan har ma da irin azabar da ake gana musu. Tsoron tafiya suke yi suna ganin ma idan sun yi gaba ma ba su san me za su tarar ba. 

Na goma sha ɗaya, akwai gado ko yanayin yadda ta taso. Ta saba da ganin ana cuzguna wa  mata a danginsu. Don haka ita ma kawai ko dukanta miji yake yi, za ta ga ai ba laifi ba ne. Domin ba sabon abu ba ne. Ta saba da ganin haka wajen iyayenta ko yayye. Hasali ma dai ta ɗauka kowanne gidan aure haka ake zaman. Don haka, duk wuya ba wani hoɓɓasa da za ta yi don ganin ta ceci kanta.

Na sha biyu, rashin sana’a da abin hannu. Matar da ba ta da abin hannunta takan dogara kacokan a kan mijinta. Idan aka yi rashin dace mijin nata na cikin rukunin waɗancan mazajen masu azabtar da mata, to ta kaɗe kuwa har ganyenta. Don ga azaba tana sha da wulaƙanci, wani zubin ma har da duka. Amma ba ta da yadda za ta fige ta gudu. Don ba ta da yadda za ta yi. Mai yiwuwa ba ta da iyaye ko ba su da ƙarfi. Ga yara barkatai kun tara. Inda za ta ajiye yaran ma aiki ne, ballantana ɗaukar nauyinsu. Hakan zai sa ta saduda ta haƙura da dukkan azaba domin rashin madafa. 

Na sha uku, tsoro. Wasu matan ba sa iya guduwa saboda tsoron abinda zai biyo baya. Wata tana jiye wa yaranta tsoro idan ta tafi ta bar su. Wata kuma har barazana yake mata cewa idan ta tafi ba za ta wanye lafiya ba. Hakan zai sa ta kasa tafiya. 

Na sha huɗu, rashin sanin makoma. Wata za ta yi ta tunanin anya idan ta bar shi za ta iya rayuwa ba shi? Anya za ta iya son wani ko wani ya so ta bayan shi? Ko kuma wa zai aure ta da tulin ‘ya’yanta?

Na sha biyar, ƙi- faɗi. Wata tana tunanin Kada ta fita daga gidan miji wasu su ga gazawarta su yi mata dariya. Musamman maƙiya ko dangin miji ko kishiya ko tsohon saurayi ko wani daban. Sai ka ga ta zauna ta shanye cin zarafi, duka da wulaƙanci.

To ina mafita?

Ya kamata mahukunta da gwamnati da malamai da shugabanni a cikin al’umma su tsaya su tsawatar. A dena cin zarafi da wulaƙanta mata a gidan aure. Ya kamata al’umma a haɗa kai a kan duk wanda yake cuzguna wa mata a dinga hana shi muƙami ko wani auren idan ya so ƙari. 

Sannan iyaye su dinga sauraren ‘ya’yansu mata da ke gidan aure su saita musu matsaloli. Ba wai kawai daga ta kawo ƙarar miji a ce ta koma ta yi haƙuri ba. Haƙurin ba shi da amfani idan ba za a zauna a duba matsalar ba. Yin haka yana nuna wa miji kuna neman kai da ita. Kuma zai cigaba da muzguna mata. Kuma gudun da kuke kada ta dawo, da wuya dai ba a yi sakin ba. Domin aure ba zai tafi ba kwanciyar hankali da fahimtar juna. 

Kuma wani lokacin rashin saurarenta ɗin zai sa ta daina gaya wa kowa. Kuma hakan zai gadar mata da ciwon damuwa (depression.)

Don Allah ku tsaya mata. Idan ma ya kama a haɗa da hukuma, ku wuce mata gaba. Ba a ce su kashe mata aure ba. Amma aƙalla  a gyara matsalar kada ta zama babba yadda shi zai iya cutar da ita ko ita ta kai bango ta yanke mummunan hukunci.  

 Sannan kuma sai al’umma sun daina }yama da zargi da dora laifi ga zawarawa laifi sannan mata za su miƙe su nema wa kansu ‘yanci. 

Ku ma mata mu nemi sana’a kuma mu rage haihuwa barkatai. 

Irin waɗannan mata, Babbar hanyar da za ka bi don shawo kansu shi ne, a zauna da su, a tattauna a fahimci matslolinsu. Sannan a warware. ba kullum fa mace ke da laifi ba. An san akwai matan da da za a biye musu sai su mai da aure ba ibada ba. A dai ƙara dubawa.

Mu haɗu a mako mai zuwa idan Allah ya kai rai.