Auren ‘yar boko!

Daga AMINA YUSUF ALI

‘Yar boko! Wannan shi ne sunan da ake kiran macen da ta yi karatu kuma take yin aiki ko take karatun gaba da Sakandare, ko ta gama, ko tana aikin albashi ko ma ba ta aikin. Wannan shi ne lissafin kuɗin goro da ke wa mace ‘yar boko a ƙasar Hausa.

Masu karatu barkanmu da haɗuwa a wani makon mai albarka! Ta cikin jaridarku mai farin jini, Manhaja. A yanzu kuma za mu tsunduma kan maudu’inmu na wannan mako.

A kan auren ‘yar boko da irin abubuwan da suke tattare da auren. Duba da yadda a ‘yan shekarun nan a ƙasar Hausa aka samu kwararowar matan aure sosai a Duniyar aiki da zurfafa ilimi ta kowanne fanni.

Wato daga boko har na Islama. Abinda yake jawo cece-ku ce a tsakanin jama’ar yankin na ƙasar Hausa.

Musamman waɗanda suke ganin wannan tamkar shige gona da iri ne, da taka shari’a da kuma raina ƙoƙarin mazajen aure da kuma gogayya da su. Amma shin wai da gaske zurfafa ilimi yana kawo wa ma’aurata tazgaro?

Akwai wani rubutu da na gani a kwanan nan da Dakta Suaiman Mai Bazazzagiya ya wallafa a shafinsa na Fesbuk da yake nuna amincewarsa da hana mata ilimi na islama mai zurfi, domin hakan yana sa idonsu ya buɗe su ƙi zaman aure.

To idan masu ilimibkamar Shaihin Malamin sun yarda da haka, ina kuma marasa shi? Maza da dama a ƙasar Hausa sun yarda da auren ‘yar boko qaddara ne kuma ba shi da wani alfanu.

To amma fa suna matuƙar son auren nata amma fa in dai ba a gidansu za ta ƙarasa karatunta ba ko kuma an yi yarjejeniya kafin auren ba za ta yi aiki ba ko za ta ajiye aikin bayan sun yi aure.

Wannan fa shi ne ana cin dankali kuma ana kushe shi. Amma ga wasu matsaloli da suke sa maza ganin auren ‘yar boko a matsayin uƙuba.

Matsalolin da maza a ƙasar Hausa suke gani a tattare da auren ‘Yar boko:

Kishi: Babban abinda yake hana namiji Bahaushe barin matarsa fita shi ne kishi. Ko daga yanayin ginin gidan Bahaushe da yadda aka jera soraye da yawa kafin a shiga ainahin gidansa wajen iyalinsa, za ka gane cewa mutum ne mai karamci saukar baki kuma mutum ne mai kishin iyalinsa. Don haka, wani kishin kada matarsa ta fita ta yi mu’amala da wasu mazan ne yake sa wa ya hana aiki da karatu. Idan kuma ya bar ta, to kishi da zargi ba za su bari a zauna lafiya a gidansa ba.

  1. Sai tsoron fanɗarewa: Wasu mazan suna ganin barin mace ta dinga zuwa aiki yana sa ta ta fanɗare ta ƙi yi musu biyayya. Domin gani zai yi za ya ba ta damar da ta wuce ƙima wacce za ta sa ta dinga yi masa kallon kansu ɗaya da shi. Musamman idan karatun da take ya zo kai ɗaya ko ya kere wanda ya yi. Ko kuma aiki take tana ɗaukar maƙudan kuɗaɗe da ta wuce ta dinga bibiyarsa don neman wani abu a wajensa. A wajen irin waɗannan mazaje, wannan zai iya zama barazana ga mulkinsu a matsayinsu na maigida, kan gida. Kuma yana ganin da wuya ya iya juya matar da take da wannan matsayi ko ya yi mata wayo. Don haka, sai zama ya qi daɗi.
    Buɗewar ido: Wasu mazan kuma suna ganin idan mace ta yi zuzzurfan ilimi ko kuma tana aiki tana samun kuɗi, to idonta zai buɗe ta raina shi ta kuma raina duk wani ƙoƙarinsa saboda wayewar da ta samu. Sannan za ta gano ‘yancinta, ta san haƙƙoƙinta ta daina yarda ana danne ta ko ta dinga tawaye idan an danne mata haƙƙi. Hakan zaiu sa kullum a kasance cikin rashin jituwa a gidansu.
    Zugar mutane: Wani kuma yana ƙyamar aikin mace ba don komai ba sai don irin kallon da al’umma za ta yi masa ko abokai ko danginsa. Za a iya yi masa kallon soloɓiyo ko wani hotiho idan ya bar matarsa tana fita aiki ko karatu.
    Rashin lokacinsa: Wata matsalar kuma mace mai aiki za a ga ba ta fiye ba da lokacinta ga mijinta ko gidanta ba kamar wacce take zaman dirshan take yi ba. Haka kuma yayin da take ba wa aikinta muhimmanci, shi mijinta zai ga kamar tana fifita aikinta a kan aurensa. Har ya zamana wani namijin ma sai ya ƙulla kishi da aikin nata. Ya yi ta jin haushi saboda yana hana shi samun lokaci. Kuma duk yadda ta so ta tsara shi dai ba zai gamsu ba. Ya riga ya ƙulla gaba da aikin kenan.
    Tauye masa haƙƙi: Idan mace tana aiki mai cin lokaci sosai musamman na kwana dole mijinta ya ji ya gani ya san wasu lokutan dole wasu haƙƙoƙin nasa ba za su samu ba. Wanda bai yarda da hakan ba, kullum suna cikin takun saƙa.
    Cin gashin kai: A al’adance namiji yana ganin shi ne jagora a gida. Kuma ko motsi mace za ta yi sai a ƙarƙashin ikonsa. Amma mace mai aiki ko karatu barazana ce a wajen namijin Bahaushe. Domin zai ga kamar tana zaman kanta ne tana yin wasu abubuwa da babu ikonsa. Shi ma wannan yana yamutsa hazon rayuwar auratayya.
    Ya gaza a idon Duniya: Namijin Bahaushe da matarsa ke aiki kullum gani yake kamar ya gaza ɗaukar nauyinta ne shi ya sa take yin aiki. Zai ta damun kansa wani lokacin ma shaiɗan ya dinga raya masa cewa tana yin aikin ne saboda tanadin rabuwa da shi. Haka dai za a yi ta samun saɓani da rashin fahimta.
    Shekaru: Haka shekarun ‘yar boko ba kamar na ƙaramar yarinyar da za a aura a bi da ita yadda ake so ba ne. Hakan zai sa ta yi wahalar sarrafuwa.
    To waɗannan wasu daga cikin dalilai ne da suke sa wa maza a ƙasar Hausa suke ganin auren ma’aikaciya ko ‘yar boko a matsayin ƙalubale. Duk da dai ana samun wasu mazan masu fahimta sosai da hangen nesa da son cigaban iyalansu.
    Amma wani gudu ba hanzari ba, me ya sa mata suke ƙara tururuwa a duniyar aiki da zurfafa karatu? Anya ba kiɗan ne ya fara sauyawa ba, sannan rawar ta sauya? Anya ba gazawar maza a ɗaukar nauyin iyali kamar zamanin iyayenmu ne ya sa mata suka bazama ba? Da ma can akwai masu sana’o’i sosai. Amma aiki da zurfafa karatun mace sabon abu ne a ƙasar Hausa. Zancen da ake ma, a da wuya in dai da dama yarinya a birni ta gama Sakandare ba ta yi ƙoƙarin cigaba ba. Wanda zamanin da iya ƙurewa, da wuya ta wuce sakandare.
    Amma abin mamakin me ya sa a ƙasar Hausa ne kaɗai aka ɗauki zaman aure da ‘yar boko abin ƙyama da tashin hankali? Shi kansa sunan ‘yar boko kamar shaguɓe ne. A wajen wasu tana nufin mai buɗaɗɗen ido ko mara tarbiyya.
    To sai dai kuma duk da kallon da ke wa ‘yar boko na rashin tarbiyya kuma dai sai ka ga idan namiji ya isa ko yana da hali ba zai je ya ɗauko irin ‘yar gargajiya. Kuma sai a ce ba za a aure ta ba sai da sharaɗin sai ta ajiye aiki ko kuma ba za ta yi aikin ba ko cigaba da karatun.
    Haka a yayin zaman aure, namiji ya fi yi wa mace mara iilimi sosai adalci da uzuri a rayuwar aure. Ko mata da dama ne da shi ya fi tausayin wacce ba ta da ilimi ko aiki ko sana’a. Saboda yana ganin ita ce ta fi dogara da shi. Wanda kuma hakan bai kamata ba.
    Haka wasu mazan sukan sakar wa nauyi da sakar mata gida da nauyin komai saboda ya ba ta damar aiki. Amma duk hakan idan ta ga dama ta ɗauki nauyin ba laifi ba ne. Sai dai kuma wata matar tana ɗaukar nauyin, kuma namijin yana gallaza mata saboda yana ganin kamar nuna gazawa ce a ce matarsa na aiki. Duk kuwa da irin tagomashin da yake samu.
    Haka wata matar yin aikin ba lallai ne shi ne zavinta ba. Kawai tana da abubuwa ko mutanen da take son ɗaukar nauyi. Takan raba rayuwarta ta karkasa kanta gida-gida don kawai ta samu daidaito tsakanin aikinta da rayuwar gidanka. Da kula da kai da yaranka.
    Haka ka dinga tunawa da cewa, iyayenta Iyayenta sun kashe kuɗi sosai don ganin ta yi karatu, ta ginu. Kai kuma ka auro ta. Ka sa kanka a matsayin iyayenta ka ga idan kai ne ya za ka ji? Haka idan aikin take yi, kafin iyayenta su more ta ɗaya kai da ‘ya’yanka kun more ta goma. Kuma kamar yadda na faɗa, ba ka son mai ilimi, tafi auri mara shi sai ku fi fahimtar juna.
    Kuma a gani na, banda abinka Yayana, ka nemi wacce ka yarda da ita kawai. Idan kana ganin ‘yar boko ta yi wayewa da yawa, to nemi ‘yar gargajiya mana. Idan ta yi maka girma nemi mai ƙananan shekaru mana. Hakan zai sa ka huta, ita ma ta huta. Hankalinka kwance ba sauran zargi.
    Haka aiki ko sana’ar mace suna sa ta fahimci kai ma irin gwagwarmayar da kake sha don ɗaukar nauyin iyali. Kuma za ta iya fahimtarka idan ba ka samun lokacin zaman gida. Domin takan samu kanta ita ma a wannan yanayi.
    Haka wajen rashin almubazzaranci. Wacce take aikin nan ta fi alkinta komai domin ita ma ta san darajar nema.
    Don haka, maza don Allah ku sakar wa ‘yar boko mara. Ita ma mace ce kamar kowacce. Tana yin kuskure kuma tana da nata alfanun. Tsana ce da miyagun ta’adoji suke mayar da ita kamar wata dodanniya a cikin al’umma.
    Kuma Yayana, wa ya san gawar fari? Duk ranar da aka ce ba ranka ita ce dai mai riqe maka yara ta kare su daga fitinar faɗawa ga lalacewar tarbiyya kamar yadda a yanzu haka muke gani marayu suke faɗawa a wannan zamani. Allah dai ya datar da mu.
    A nan za mu tsaya sai wani makon idan rai ya kai. Muna godiya ga masu tuntuvarmu ta waya, su yi godiya, addu’a, tsokaci har ma da ba da shawara. Haƙiƙa kuna ƙarfafa mana gwiwa.