Auri-saki a ƙasar Hausa: Laifin wanene?

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a filinku na Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan makon za mu yi magana ne game da auri-saki a ƙasar Hausa. Ko ba a gaya maka ba mai karatu za ka yi wa kanka alƙalanci cewa ƙasar Hausa tana neman zama shalkwatar mace-macen aure a Nijeriya. Domin idan ka dubi sauran ƙabilu, ba su fiye samun wannan matsala ta saurin mutuwar aure da sakewa ba kamar yadda muke yi a nan yankin.

A ‘yan kwanakin nan ma da aka yi ta zance game da halayyar jarumi Adam A. Zango na auri-saki, inda wasu suke ta zafafan musayar yawu tsakanin ɓangarorin da ke ƙoƙarin ganin sun kare shi da kuma wasu ɓangarorin da suke ganin rashin kyautawarsa.

Wannan ya sa na yi nazari a kan wannan ɗabi’a wacce kusan ta zama ba wani abin mamaki ba ne a ƙasar Hausa. Ba tsoho ba yaro, kuma ba mai kuɗi ko talaka, ko malami ko jahili. To me yake kawo haka a ƙasar Hausa?

Da farko dai, shi sakin aure ba a ce laifi ba ne. Tunda musulunci yadda ya shar’anta aure haka ya shar’anta sakin aure. Duk da dai wani hadisi ya bayyana mana cewa, daga cikin abubuwan da Allah ya halatta kuma yake tsananin ƙi shi ne, sakin aure.

Shi ya sa ya kamata ma ɗanuwa ya duba tare da cizawa da busawa idan matsalar ba fin qarfi ta yi ba a haqura da sakin. Domin idan ka kasa haƙura ma dai wata za ka aura. Kuma ita ma dole ne ka yi haƙurin da ita, ko ka sake ta a dinga ƙirga maka aure. Dalilan da ke sa namiji yin auri-saki:

  • Ƙaddara: Da farko akwai ƙaddara. Ba wani abu ne ya sa na kawo ƙaddara ba illa sanin cewa, akwai waɗanda an riga an ƙadarta za su yi aure-aure a rayuwarsu. Za ka tarar irin waɗannan mazan ba wai muhun halinsu ko na matansu ba ne yake raba auren ba, illa ƙaddara. Za ka ga ya auri waccan, qaddara ta sa an rabu sannan ya sake aure wata kuma daban. Haka dai.

*Rashin dace/bauɗaɗɗen hali: Akwai wasu mazan masu bauɗaɗɗen hali waɗanda ba kowaccce mace ce za ta iya jure ta zauna da irin halayyarsu ba. Wasu lokutan akan samu wata wacce za ta fahimci halinsa sosai, sai a ga ita kaɗai ke iya zama da shi, amma duk wacce ya auro sai ta fice. Wannan yana janyo zargi a dinga ganin ko ita matar ita ke korar sauran matan da ake aurowa. Nan kuwa babu ɗaya bare ƙanwar biyu. Kawai halayyarsa ce take korar matan.

*Zafin rai/rashin haƙuri – Akwai mazan da su kuma tsabar zafin rai da rashin haƙurinsu ya yi yawa. Abu kaɗan mace za ta yi su ce sun sake ta. Haka zai ta aura yana saka saboda rashin haƙuri. Sai tsufa ya cim masa sannan zai gane illar hakan.

*Kwaɗayi: Wasu mazan kan yi auri-saki saboda kwaɗayin abin duniya. Duk inda ya ji ga wata mai dukiya ko mijinta ya mutu haka ya lallava ya aura don ya samu ya ci arzikinta. Idan sun cinye ya saita mata hanya ya nemi wata mai maiƙon.

*Auren ɗanɗano wasu mazan kan auri mace budurwa ko bazawara saboda su ɗanɗana ta su sake ta. Galibi irin waɗannan mazan da zarar mace ta samu ciki, ta gama fita a ransu. Daga nan za su fara wulaƙanta ta daga ƙarshe dai a rabu, ɗan ma a gidan iyayenta za ta haife shi. Wani kuma sai ta haihu yake saita mata hanya. Irin wannnan aure masu abin hannunsu wato masu kuɗi su suka fi yi musamman waɗanda ba su da ilimin boko da na addini sosai.

*Neman haihuwa – Wannan auri-saki waɗanda suka fi yi su ne masu kuɗi da sarakuna ko malamai da suke neman magada da makamantansu. Irin waɗannan mutane sukan auri mace yau, bayan ‘yan shekaru idan ba ta yi ciki ba, su auri wata. Haka za su cika gidajensu da mataye.

Su auri wannan, su auri waccan wai duk da nufin a dace da samun haihuwar. Idan kuma matan suka cika huɗu shi ma sai su saki wata ko wasu daga ciki, su kuma maye gurbinsu da wasu. Haka dai.

To waɗannan su ne wasu daga dalilan da suke sanyawa a yi auri-saki. Sai dai kuma abinda yake ba da mamaki yadda su waɗannan masu auri-saki suke sake samun wasu matan su aura ba tare da wahala ba duk kuwa da cewa sun auri wasu sun sake su a baya. Wasu ma ya zama ɗabiar su.

Kuma al’ummar suna gani. Wasu ma fa maƙwabtansu ne za su ba su aure. Kamar misali a kes ɗin jarumi Adam A Zango yadda ya yi suna ya yi shuhra kuma kowa ya san labarin abinda ya faru da shi na aure, amma duk da haka wannan bai hana a ba shi yarinyar da zai aura ba.

Duk da dai ban yi binciken da zan gano waye mai laifi tsakaninsa da matan nasa ba. Amma abin mamaki ne matuqa. To me yake faruwa? A ƙasar hausa ne fa kaɗai mutum ya auri-saki ya zauna lafiya.

Akwai ƙabilun da a ƙasar nan fa idan aka ce mace aurenta ya mutu shikenan da wuya ta kuma samun wani ya aure ta. Sannan kuma namiji shi ma idan yana sakin aure shi ma da wuya a sake ba shi aure. Shi ya sa za ka ga su matsalar auri-sakin kaɗan ce a kan tamu.

A ƙasar hausa akwai dalilai da dama da ya sa ake yin auri-saki da kuma dalilan da suke sanyawa masu auri-sakin ba sa dainawa. Za mu kawo muku wasu daga cikin dalilan a wani makon idan Allah ya kai rai. Masu karatuna da masu kiran waya muna godiya da ƙarfafa mana gwiwa da kuke yi. Allah ya bar zumunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *