Ayyururui! An buɗe waya a Gusau

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Sai albishir da sambarka mutane ke yi wa juna biyo bayan buɗe na’urar sadarwar salula a Gusau, jihar Zamfara. Wannan na nuna aƙalla dai mazauna fadar gwamnatin jihar za su iya buga waya da hawa dandalin sadarwa. Sauran yankunan jihar dulum su ke ta wannan fuska don matakin gwamnati na datse sadarwa da zummar murƙushe ɓarayin daji.

Irin wannan lamari ya na da riba kuma ya na da akasin haka. Don alamu na nuna yayin da a ke da ɓarayin daji akwai ɓarayin birni. Wannan ba zai zama abun mamaki ba don an nuna wani jami’in tsaro da a ka cafke da ke taimkawa ɓarayin daji.

Kazalila gwamnatin ta ba da labarin cafke masu tseguntawa ɓarayin daji halin da a ke ciki don kaucewa yi mu su ƙofar rago. Dama yadda wannan lamari ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ai da walakin goro a miya. Abun da a ke gani a zahiri shi ne yayin da ɓarayin daji ke hallaka mutane a ƙauyukan su da kwashe dukiyar su ko sace mutane da karɓar kuɗin fansa; wasu ‘yan-sa-kai ko ‘yan banga kan yi wuf su yanka wani Bafulatani da ya shigo kasuwa da a ke zargin ɓarawon daji ne.

To ashe yayin da hakan ke faruwa a na kulle gida da ɓarawo ne don ba mamaki a kasuwar akwai ‘yan tsegumi sun yi likimo su na farautar labarin da za su tura daji. A gaskiya wannan aiki ne gagarumi na yaƙi da mutanen da ke zaune a cikin kasa koma a boye a cikin jama’a. Kun ga yaƙi tsakanin wannan ƙasa da waccar da sauƙi don kowane ɓangare ya san inda zai shata daga.

Gabanin dawo da sadarwar Gusau, na ji labari mutane kan biya motoci su nufi Zaria ko Sokoto don buga waya. Wannan ya nuna a zamanin yau mutane ba za su iya rayuwa mai ma’ana ba sai da taimakon kimiyya da fasaha. A can baya ai an yi wayar girke ta hukumar sadarwa NITEL amma da ya ke sai gidan Alhaji wane ko Sarki wane ai jama’a ba su damu ba.

A lokacin karin maganar nan ta Hausawa ‘zumunta a ƙafa ta ke’ ta yi tasiri. Don in ka na da niyyar sada zumunci sai ka tashi takanas ta Kano ka nufi garin su wanda ka ke son gani don ku gana. Hakanan a lokacin hukumar gidan waya na da tasiri don rubutawa da aika wasiƙu ta hanyar zuwa gidan waya a sayi kan sarki a lika, a tsawon mako biyu in an dace sai a samu amsa. To yanzu fa? Ai ka ga waya ba wata hajar gabar ba ce don yayin da wani zai sayi ta kusan Naira miliyan ɗaya ya buga waya hakanan wani talaka zai sayi tsohuwar waya ta Naira dubu biyu ya buga waya shi ma.

Kuma an ce biyan buƙata ya fi dogon buri. Da dalilin kashe sadarwar salula, yanzu an fara yaɗa cewa varayin daji na amfani da wasiƙar takarda wajen buƙatar kuɗin fansa. Wannan gaskiya ko akasin haka, jami’ai da gwamnati da a kan ji bayani daga gurin su na cewa yaƙin ya cimma nasara. Shi kuwa talakawa kan ce sai ya gani a ƙasa ko sai ya daina jin a na kai har wasu ƙauyuka ko ma dai sai an daina zubar da jini ba bisa haƙƙin shari’a ba. Ko ba fitina ta shiga arewa ba, yaushe a ka taɓa mafarkin jama’ar gari za su yi kukan kura su cafko miyagun iri su banka masu wuta su ƙone ƙurmus kuma su na ɗauka da waya su na murna su na yaɗawa duniya namijin ƙoƙarin da su ka yi.

LallAI kuwa akwai buƙatar zaman lafiya a duk birane da ƙauyukan Arewa da hakan ba zai gama samuwa ba sai hukumomi da duk jama’a sun rungumi adalci, gaskiya da rikwan amana. Adalcin nan ba sai daga shugaban ƙasa ko gwamna zuwa kansila ba, hatta mai sayar da mangyada da manja a kasuwar ƙauye sai ya kaucewa algus. Matuƙar mutane za su rayu a yanayin tara abun duniya ko neman na abinci ta kowane irin hali, to haƙiƙa zaman salama ba zai tabbata ba. Kuma matuƙa akasarin talakawa za su zama masu cin amanar juna ko da ta hanyar zunɗe da nune ne bare ma a je ga maganar sata, zina, luwadi, maɗigo da kisan gilla; to za a cigaba da samun azzaluman shugabanni da fitintinu marar sa magani na kusa.

Bayanan jami’an gwamnatin Nijeriya kan nasarar da a ke samu wajen yaƙin ‘yan ta’adda da sauran ‘yan bindiga daɗi, na saɓawa da irin bayanan da mutanen karkara ke yi. Hakan na nuna ma’aunin nasara na gwamnati da na jama’a na da bambanci. Kamar taƙaddamar wannan ya ce, shida ne, wancan ya ce a’a tara ne, kuma ba mamaki in duba kowa ya na da gaskiya in an duba daga inda ya tsaya ya na kallon lambar ko yanda lamura ke gudana.

Yayin da gwamnati ke cewa dakarun tsaro na birkita lissafin miyagun iri, jama’a na cewa miyagun na sauya dabarar halaka jama’a ne da mallake dukiyarsu.

“Yanzu mu kan kai farmaki ne ga maƙiyanmu har inda su ke kuma a cikin watanni huɗu da su ka wuce zaratan jami’an tsaron mu sun samu gagarumar nasara” inji shugaba Buhari a sashen jawabinsa na ranar ‘yancin cikar Nijeriya shekaru 61 da samun ‘yanci daga turawan Burtaniya. Shugaban ya nuna murna cewa baya ga nasarar da ya ce jami’an sun cimma, kazalika fiye da ‘yan Boko Haram 8000 su ka yi saranda a arewa maso gabar.

wannan duk da wasu da ke Borno na zullumin zama da tsoffin mashaya jini da wataqila waɗanda an san mutanen da su ka yi wa yankan rago.

Shugaban ya ce, rundunar soja ta na ɗaukar sabbin jami’ai yayin da ya ba wa rundunar ‘yan sanda umurnin a duk shekara har tsawon shekaru 6 ta riƙa ɗaukar sabbin jami’ai dubu 10. Duk da in an bincika za a ga wasu da a ka ɗauka ka iya zama baragurbi ko kuma wasu an ɗauke su ne don su na da wasu da su ka tsaya mu su a gwamnati ko a manyan ‘yan siyasa. Kazalika zai iya yiwuwa wasu sun ba da bayanan bogi a lokacin ɗaukar su ko amfani da sunan jihar da ba ta su ba wajen neman aikin a tsarin nan na a samu aiki kawai. Wasu ma ba sa kishin ƙasa sai ƙabila ko yankin su amma sai ka ga ba mamaki an ɗauke su aiki sun fito sanye da kayan sarki don kare muradun da su ka yi hannun riga da na tarayyar Nijeriya.

Mutane a jihohin da musamman a ka datse layukan sadarwa, na nuna buƙatar sauya dabara daga jami’an tsaro. Mansur Abubakar shugaban wata ƙungiya ce mai taken zaman lafiya da adalci “Peace and Justice” a Arewa-maso-yamma; ya ce rufe layukan waya na da riba da akasinta, don a yankin Sokoto miyagun sun shiga amfani da layukan sadarwa na jamhuriyar Nijar.

Aƙalla dai gwamnatin Zamfara ta dawo da sadarwar salula a Gusau, inda mutan Munya a Neja ke cewa su ma a bi kadunsu don miyagu kan yi kisa a yankin ba hanyar ankarar da jami’ai.