Azumin Ramadan: Cibiyar Saudiyya za ta ciyar da ’yan Nijeriya 12,600

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Cibiyar Agaji ta Sarki Salman da ke ƙasar Saudi Arabiyya (KSrelief, Abibakr As-Sidiq Philanthropic Home) ta bayyana cewar, za ta ciyar da ‘yan Nijeriya da abinci a wannan wata na Sharu Ramadana da ɗaukacin Musulmin duniya suke jiran isowar sa.

Shirin tallafin na Sarki Salman ‘KSrelief’ a ranar Alhamis 24 ga watan Fabrairu, 2022 ne ya sanya hannu da Cibiyar Taimako da Agaji ta Ƙasar Saudiyya domin ya raba kwandunan abinci wa magidanta guda 2,300 a Nijeriya, a cikin watan Ramadan mai gabatowa.

Shirin na agajin zai ciyar da Musulmi ‘yan Nijeriya kimanin dubu 12, 000 waɗanda suke cikin ƙangin talauci da samun abun kaiwa bakin salati zai yi masu matuƙar wahala a lokacin na watan azumi.

Masu cin gajiyar wannan shiri, har ila yau, za su kasance ne waɗanda illar ƙarancin a Nijeriya kayi nuni shara-shara a jikkunan su.

Ƙananan hukumomin jihohin Kwara da Kano, harɗe da ɗimbin masu gudun hijira da suke maƙare a birnin tarayya ta Abuja ne ake sanya ran suci gajiyan wannan tallafi ta ƙasar Saudiyya.

Wakilan cibiyoyin agaji na ‘KSrelief’ da ‘ASPH’ dake Abuja ne, Mista AbdulKarim bin Abdulmohsen Al-Yousef da Mista Sultan Mohammed Saleh, suka wakilci mataimakin shugaba kan ayyuka na musamman na cibiyar Abibakr As-Sidiq daya shi ma ya wakilci shugaban gidauniyar, suka halarci wajen sanya hannu na bayar da tallafin.

Abdulrazzaq, wanda mataimakin sa ya wakilta, ya nuna godiyar sa wa KSrelief bisa ƙoƙarin ta na kawo wannan tallafi zuwa Nijeriya, la’akari da yadda mutane masu yawa a ƙasar suke ta karakainar ci da ciyarwa.

Ya yi la’akari da cewar, Nijeriya tana fuskantar matsanancin tattalin arziki, lamarin da ya sanya wasu jama’ar ta ke wahalar neman ababen rayuwar yau da kullum, yana mai bayyana ƙarfin gwiwar mutane masu yawa za su amfana daga wannan tallafi.

Ya kuma bayyana godiya wa jama’ar ƙasar Saudiyya, waɗanda ya lura da cewar, jajirtattu ne wajen samar da tallafi wa mutane a sassa daban-daban na duniya.