Baƙin haure 39 sun mutu a Tunisia

Daga FATUHU MUSTAPHA

Aƙalla baƙin haure 39 ne suka rasa rayukansu a lokacin da kwale-kwale biyu suka nitse a kusa da Tunisia a ranar Talata yayin da suke ƙoƙarin tsallake kogin Bahar Rum zuwa tsibirin Lampedusa na Italiya, in ji jami’an tsaron Tunisia.

Jami’in Tunisa Mohamed Zekri, ya ce masu tsaron bakin ruwa sun samu nasarar ceto wasu mutum 165, sannan ana ci gaba da neman ƙarin waɗanda suka tsira a gaɓar Sfax.

Ya ƙara da cewa dukkan baƙin hauren da suka mutun ‘yan Afirka ne.

Jaridar Alarabiya ta ruwaito cewa, a 2019 kimanin baƙin haure ‘yan Afirka su 90 ne suka nitse a ruwa a lokacin da kwale-kwalensu ya kife a gaɓar tekun Tunisia bayan da suka tashi zuwa Turai daga maƙwabciyarta Libya, a ɗaya daga cikin haɗurran da suka faru.

Wata ƙunkiyar kare haƙƙin ɗan-Adam ta ce adadin baƙin haure ‘yan ƙasar Tunusiya da suka sauka a gaɓar ruwan Italiya ya ninka har sau biyar zuwa 13,000 a shekarar 2020, tana mai danganta ƙaruwar adadin da matsalar tattalin arziki a Tunisia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *