Ba a amfani da tsarin dimukraɗiyya a zaɓukan Nijeriya – Gambo Danpass 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Basaraken ɗan kasuwa kuma ɗaya daga dattawan Arewa, Alhaji Gambo Abdullahi ya yi kira ga Shugabanni da sauran talakawa akan cewa  abinda ya kamata su yi musamman da lokacin da ake tunkarar zaɓen 2023 ke matsowa shine su yi adalci, kuma al’ummar arewa duk  wanda ya sake ya  yar  da nasa neman mulkin ƙasar nan kafin ya lalubo shi zai wahala, don haka al’ummar arewa su sani nasu dai shine nasu.

Ya ƙara da  bayyana yadda aka samu kai a halin yanzu a dimukraɗiyya da abubuwa ke tafiya ba daidai ba, musamman ta yadda ake ta haddasa gaba da fitina da  komai girman mutum bai wuce cin mutunci ko wulaƙanci ba; hakan ba ƙaramin abin takaici ba ne.

Ya ce su abinda suka sani a dimukraɗiyya, shine a gina al’umma a samar musu da madogara ta sana’ar yi, amma a cewarsa yanzu yawancin gwamnatoci a ƙasar nan ba abinda suka sa a gaba sai wasu abubuwa na daban.

Ya ƙara da cewa in aka duba irin kuɗaɗe da gwamnati ke samu daga haraji da mutane ke biya, amma sai ka ga ba a ƙoƙari da za a samawa mutane abin yi daga ciki.