Ba a koyon rubutu, ba a sayen sa da kuɗi – Jamila Rijiyar Lemu

Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu ƙwararriyar marubuciya ce da ta daɗe tana jan zaren ta a duniyar rubuta littattafan Hausa.  Kuma ta yi zarrar zuwa ta biyu a gasar da sashen Hausa na BBC ke shirya wa mata zalla a duk shekara, wato ‘Hikayata,’ a shekarar 2019. A wannan tattaunawar da wakiliyar Manhaja, za ku ji yadda marubuciyar ta sha gwagwarmaya da faɗi-tashi a harkar rubutu.

Daga AISHA ASS

Mu fara da jin tarihin ki a taƙaice.
Bismillahir Rahmanir Rahim! Suna na Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu. An haife ni a shekara ta 1980. Na yi karatu tun daga firamare zuwa Jami’ar Bayero ta Kano inda na yi karatu a tsangayar ilimin tattara bayanai da adana su (Library and Information Science) matakin digiri. Ina da ‘ya’ya shida, uku mata, uku maza.

A wace shekara ki ka fara rubutu?
Na fara rubutu a shekara ta 1989, a lokacin da na ke ‘yar shekara tara ina aji 2-3 a Firamare.
 
Ya sunan littafin ki na farko?
‘Idan Ba Ka Ci Naman Kura Ba..’ shi ne littafi na na farko da na fara rubutawa, amma ban samu buga shi ba duk da cewar littafin ya samu dubawa a wajen ƙwararre kuma masanin harshen Hausa wato, marigayi Mal. Abdullahi Sani Makarantar Lungu (Allah Ya gafarta masa amin). Dalilin da ya hana na buga shi ne, lokacin da na rubuta littafin duba da shekaru na, babu wanda ya bi ta kan littafin a gidan mu, ni dai ban fasa ba haka na ci gaba da rubutu na da na gama na ajiye har zuwa Sakandare ban daina ba, domin haka na ci gaba da rubuta wani sabo. Bayan na kammala Sakandare lokacin ina da shekaru 15 zuwa 16 aka yi min aure. Sai da na haifi yara biyu sannan na fara ɗab’i, to ganin cewa littattafan da na  rubuta ina Sakandare hankali da tunani na ya na gaba da na sanda na ke Furamare, shi ya sa ban buga shi ba, kawai na fara da na bayansa duk da cewar dai shi ma littafin da na fara rubutawar ya samu yabo daga ƙawaye na da kuma wanda ya duba shi da yi masa gyara, na ƙa’idojin rubutu da nahawun Hausa, a bayan gama Sakandare kenan. Wani abu da ya ƙara min ƙaimi a harkar rubuce-rubuce na, ba na mantawa da tattaunawar mu da marigayi Mal. Abdullahi Sani Makarantar Lungu lokacin da ya ke duba littafi na ‘Idan Ba Ka Ci Naman Kura Ba..’ duba da shekarun da na yi rubutun inda ya ce da ni “Da kyau! Kamar ki kin san zamantakewar rayuwa har ki ka yi rubutu akai?”

Sai dai na sunkuyar da kai na ce “Na’am! Malam”. Sai ya ƙara tambaya ta mene ne jigon littafin nawa?
Na ce masa “Soyayya!” Na faɗa ina daɗa sunkuyar da kai ya na murmushi ya ce “Madalla sai dai ka da ki kuskura na ga saurayi da budurwa su na taɗi a lambu a cikin littafin ki, domin wannan ba al’adar Bahaushe ba ce”. Ni ma na yi murmushi tare da amsawa “Haka ne Malam.”

“Yawwa yanzu bari na tambaye ki a matsayinki na marubuciyar Hausa ko za ki iya gaya min jimlar Ɓauna da daidaitacciyar Hausa?” Cikin sauri irin na sani ɗin nan na ce, “Ɓaunoni!”
“A’a ba ki faɗa daidai ba” Na sake azamar magana, “Ɓaunaye!” ya girgiza kai ya na murmushi, “Ba haka ba ne” Na yi shiru ina tunani ya ce “Kin ba ni gari?”
“Na’am Malam” Sai ya ce, “Ɓakwane!” Take na fahimci lallai Hausa ba dabo ba ce! Na kuma gane da akwai aiki a gaba na duk da ina ganin Hausar yare na ce.

Ya aka yi ki ka samu kan ki a duniyar rubutu?
To ni dai a wannan gaɓar abin da zan iya cewa ko na sani shi ne, lokacin da na ke Furamare akwai yayan mu da ya ke koya mana karatu a gida a mafi yawan ranakun ƙarshen mako. Wata rana da yamma bayan mun kammala darasi sai na ɗauki littafin rubutun sa ina dubawa a nan na yi gam-da-katar da rubutaccen labarin wasan kwaikwayo, kawai sai ƙwaƙwalwa ta ta fahimci shi ne ya ƙirƙiro ya rubuta, duk da ƙarancin shekaru na sai ban yi ƙasa a gwiwa ba na ce, “Yaya Nasir da kan ka ka rubuta wannan labarin?” Ya amsa min, “Eh! Ni na rubuta kaya na”  Take kawai na ji a raina ni ma zan iya saƙa zaren labari da kaina na rubuta”. Na ce, “Ni ma fa Yaya Nasir zan iya rubuta labari kamar haka”. Nan da nan ya dube ni ya na murmushi “Ma sha Allah! da kyau haka ake so”.  Ba da vata lokaci ba ya ba ni kuɗi, “Maza sayo littafi ki rubuta” Na karɓa cike da murna da annushuwa na sayo na kuma fara daga lokacin cikin ikon Allah amma kuma shi ɗin ko dai ya ci gaba da yi, to bai taɓa wallafa littafi ba sannan bai taɓa ce min yaya, ƙaƙa? Balle kanzil game da rubutu na ba, sai dai kawai ya ga ina bugawa kuma ya na yaba min da jinjina min sosai, haka ni ma ban taɓa masa magana a kan nasa ba har wa yau kuwa.

Za mu iya sanin adadin littattafan ki?
Littattafai guda goma na rubuta, bakwai a kan zamantakewar rayuwa, ɗaya kuma na tarihi, sai biyu kuma ban wallafa su ba suna nan ajiye.
Waɗanda na yi ɗab’in su su ka shiga kasuwa su ne; ‘Kanya Ta Nuna…1 2 & 3, ‘Zaki Da Maxaci’ 1 2 & 3, ‘Shan Koko..’ 1 2 & 3, ‘Mamaya 1 & 2, ‘Tattabara 1 2 & 3, ‘Cizo Da Kamar Ceto 1 2 & 3’, da kuma ‘Bakin Ganga 1 & 2, ‘A Daidaita Sahu: Tarihinta Da Ayyukanta 2004-2007. Waɗanda kuma ban wallafa ba; ‘Idan Ba Ka Ci Naman Kura Ba’,  da ‘Tsaka Mai Wuya’.

Ki na karanta littafan wasu marubuta?
Ba kasafai ba amma dai na kan karanta na wasu waɗanda kwanyata ta yaba da ƙwaƙwalwar su. Batun kwaikwayo sam ba ɗabi’ata ba ce kuma ba na son haka ko kaɗan, domin babu hikima ga hakan shi ya sa idan na yi rubutu ko zan yi sai na tambaya an tava irin haka ko makamancin sa? Da zarar an tava take na ke sauya layi hatta sunan littafi idan na saka muddin na ji wani ya riga ni kafin na fitar, canzawa na ke yi kwata-kwata kuma ko a cikin labari ne idan na ji ko na ga na samu haɗewar basira muddin ban riga na fitar ba sai kuwa na san yadda na yi na gyara nawa domin babu hikima ga haka musamman maimaita abin da aka riga aka yi duk marubuci da ya amsa sunan sa kamata ya yi komai nasa ya kasance nasa ne, shi ya zauna ya ƙirƙiri kayan sa, duk da an sani ana samun gwaruwar tunani da hasashe ɗaya amma irin wannan a bayyane ya ke da an gani babu tantama ko hasashen kwafe. Sau da yawa idan rubutun marubuci ya birge ni to ƙoƙari na ni ma na ƙirƙiri nawa daban ba wai na bi salon nasa ba, ni a waje na hakan ci baya ne gaskiya saboda kama da wane aiba wanen ba ce kawai ka zama kai ɗin.

Ya alaƙar ki ta ke da marubuta yan uwan ki?
Ina da kyakkyawar alaƙa da kowa, marubuta duk inda su ke ina girmama su ina girmama baiwar su, domin na san rubutu wani abu ne da ba kowa Allah ya ke bai wa ba kuma ba a iya saya da kuɗi, duk da cewar ana koyon rubutu ta hanyar karatu kamar yadda wasu ke faɗi kuma na ga kamar ma wasu marubutan a yanzu su na buɗe wasu kafofi na koyar da yadda ake rubutun littattafai to shi kansa koyon sai mai baiwar iya koyon ya kan iya koyon, don haka ina jinjina ga dukkan ɗaukacin marubuta masu rubutun tsafta. Ni ‘yar ƙungiyar ANA ce reshen Jihar Kano wadda ta game maza da mata duka kuma masu rubutun Hausa da Turanci, sai dai duba da ciyar da Adabi gaba ina nan ina duba wata ƙungiyar rubutun Hausa zalla na shiga cikinta domin haɓaka harshen Hausa da ci gaban su in sha Allah.

A ganin ki fitowar Online Writers ci gaba ne ga Adabi ko ci baya?
Duba da zamani ba za a ce babu ci gaba ko kaɗan game da online writers ba, sai dai rashin amfanin su ya yi wa amfanin su zarra matuƙa gaya, domin a yanzu dai ina ganin ci baya ne ga Adabi kai har ma ga tarbiyyar yara bisa irin baɗalar da wasun su ke tabkawa a kafafen sadarwa kuma da sunan marubuta Hausa a jam’iyyance, gaskiya wannan ba ci gaba ba ne kuma ba zai haifar da ɗa mai ido ba, muddin aka ci gaba da shiga irin wannan riga mai daraja ta rubutu da ake yi wa kirari da ‘Alƙalami Ya Fi Takobi’ da zummar gina al’umma kacokan, wannan abin takaici ne da kaicon gaske na samuwar irin waxannan marubutan baɗalar da su ka yi sansani a duniyar online. Kodayake a matsayin mu na ɗaliban Adabi Farfesa Malumfashi ya ce “Kowane tsuntsu da jinin gidan su yake tashi! A cikin ire-iren rubutun marubuta akwai na gado da jini” Jin haka ni kuma na gamsu yayin da ƙwaƙwalwata ta hakaito min tabbas ‘A karin ruwa ne ake yin kwashe, ko wane iri mutum ya ɗebo zai iya tafasawa ya sa siga da gishiri ya sha kayan sa, amma jini sai irin naka, saboda haka sai dai mu ce Allah Ya shirye su da mu bakiɗaya Ya kuma sa su gane gaskiya gaskiya ce su daina amin, saboda babu abin da irin wannan rubutun na baɗala zai haifar face rugurguza Adabi. Maganar rubutu a littafi ba ƙarama ba ce tilas su zama bayyanannu shi  ya sa su ka ɓoye kansu a online su ke shan sharafin su, to amma fa su sani idan sun ɓoyu ga mutane ba za su voyu ga Allah ba, Ya na nan ya na kallon su kuma ba zai ƙyale su ba akwai hukunci bisa kansu, muddin ba su tuba sun daina ba. Bisa gaskiya rubutu a littafi ya fi ciyar da Adabi gaba saboda rubutu rayayyen abu ne kuma ta hanyar sa tarihi ya ke dawwama Allah Ta’ala Ya yi rantsuwa da Alƙalami a cikin Alƙur’ani mai girma haka Annabi SAW ya umarce mu a kan rubutu domin in aka yi shi komi daren daɗewa ya na nan a yadda aka yi shi, don haka rubutu ya na da daraja sosai kuma muhimmin abu a cikin rayuwa. Alƙur’ani maigirma ya isa hujja domin a rubuce mu ka gan shi. Shi ya sa ni dai ina girmama dukkan rubutu mai tsafta.

Kin taɓa rubuta fim?
Eh! Na rubuta fina-finai guda uku; ‘Yanci, Taskar Rayuwa da Mati A Rufta.

Akwai wa ta nasara ko nasarori da ki ka samu ta sanadiyyar rubutu?
Nasara babba ma kuwa saboda sanadin rubutu aka ɗauke ni aiki a Hukumar A daidaita Sahu har na zama ma’aikaciyar dindindin a ƙarƙashin Gwamnati bayan an yi wa hukumar doka, saboda shirin ya ƙunshi faɗakarwa da kuma wayar da kai ne, bugu da ƙari hakan ne ya ba ni damar ƙaro ilimi na digiri, sannan na yi gogayya da manyan ƙwararru masana na gida da na waje, ƙasashen ƙetare, baƙar fata da farar fata. Na bai wa mutane da yawa waɗanda ban san iyakar su ba shawarwari a kan matsalolin su ta waya da ƙafa da ƙafa. Na yi workshops da seminar da manyan ƙungiyoyin ci gaban al’umma da kuma  wayar da kai irin su; DFID, SJG, British council da sauran su. Har wa yau rubutu ne sanadin da ya sa na samu karramawar BBC a gasar gajerun labarai ta mata zalla wadda sashen Hausa na BBC Hausa su ke shiryawa duk shekara wato ‘Hikayata’ inda na samu nasarar zama gwarzuwa ta biyu da labari na mai taken ‘Ba A To Komai Ba.” A shekarar 2019.

Ƙalubale fa?
Haƙiƙa ƙalubale akwai su domin babu yadda za a yi a ce mutum bai yi karo da su ba a cikin al’amuran rayuwar sa. Na sha wahala sosai sanda na fara buga littaf ina ‘Kanya Ta Nuna’ tun daga typesetting zuwa shigar sa kasuwa inda aka riqe min kuɗi na su ka kai wani lokaci mai tsawo ba a ba ni ba, duk da cewar littafin ya ƙare tuni a kasuwa, amma ba uwar kuɗin ba riba ba kuma kayan a ƙasa, kai har da N200 aka riƙa  biya na bayan na sake bugawa domin ban daddara ba. Lokacin da zan fitar da ‘Zaƙi Da Maɗaci’ ma haka na sha wahala domin ta kai har ina tafiya ina kuka kafin littafin ya haɗu saboda takaicin na biya kuɗi na tsaf na aikin ɗab’i duka, amma aka riƙa yi min yawo da hankali, irin na ajin ƙarshen rainin hankali, kodayake an ce inda fata tafi laushi a nan ake mai da jima. A taƙaice kusan dukka littattafai na a harkar bugu da kasuwancin na wahala da guntu-guntu aka riƙa biya na wani ma sai bari na yi kawai na haƙura, ga rashin girma da dattaku da jeka-ka-dawo na mafi yawan ‘yan kasuwar Adabi, mutum ɗaya ne na ji daɗin sa daga baya-baya wanda Allah Ya dube ni ya haɗa ni da shi wato, Malam Sadisu Musa Mandawari, Allah Ya jiqansa ba don ya mutu ba shi kaɗai na samu sawaba hannun sa.

A na ki hange me ya janyo lalacewar kasuwar Adabin Hausa?
Hmm! Idan ana Sallah ba a magana, bari na tafi kaitsaye bisa gani na da hujoji na, son kai da son zuciya da rashin amana ne matakin farko na durƙushewar lalacewar kasuwar Adabin Kano. Da yawa ‘yan kasuwa kansu kawai su ka riƙa ginawa su ka riƙa juya kuɗin marubuta ta wata fuskar su na kasuwanci domin na ji da yawa su na faɗin har Dubai wasu su ka riƙa fita, bayan bayyanuwar haka jikin marubuta ya yi sanyi su ka riƙa ja baya a harkokin rubutu tare da fafutukar yadda za su karvi haƙƙoƙin su. Kafin nan akwai son zuciya ƙarara da ‘yan kasuwar littafi ke yi idan su ne su ka ɗauki nauyin buga littafi ko su na da alaƙa da marubci ko da littafin sa bai kai daraja ba to nasa ko na su su ke cusawa masu sari idan sun zo daga cikin gari ko wasu garuruwan wasu ma a kan idon su za su ga haka, ko ni ma an yi haka a gabana, to a nan marubuci ya kawo Littafin sa kasuwa, bayan lokaci mai tsawo ya dawo karvar kuɗi an nuna masa tarin littattafan sa a ƙasa, gobe haka, jibi haka tilas ya karaya sha’awa da ra’ayin rubutu ya fita kansa, to wannan ma ya taimaka wajen lalacewar harkar kasuwar Adabin Kano. Sai kuma yanayin halin da kasarmu ta shiga na rashin kwanciyar hankali wanda hatta harkokin kasuwanci  sai da ya taba kiwa ya san wannan saboda haka ana ta kai wa yake ta kaya? Wannan ma ya kara haifar da durqushewar kasuwancin Adabi kacokan sannan akwai harkar matsalar waya ma ciki ita ma ta taimaka mutane da son sauƙi su na ganin su na zaune a gida za su latsa ta su yi yawo a ko’ina cikin duniya a kanta, shi ma karatun littafin ana yi a kanta, to me zai hana ci gaba a ruƙurƙushewar kasuwar Adabin Kano?

Wasu su na ganin rashin haɗin kan marubuta ne ya durƙusar da rubutun Hausa, shin me za ki ce?
Haka! Domin kowace cuta ta na da magani haka dukkan matsala ta na da maslahar ta. Haƙiƙa  marubuta ma su kishin rubutu da jin ciwon  durƙushewar rubutun Hausa sun yi ƙaranci a wannan zamani, tabbas da a ce akwai jajirtattu sosai da kuma haɗin kai matuƙa to da tuni an haɗu an yi taron dangi an yi wa wannan tubkar baƙar saƙar warwara, domin tayar da Adabin Hausa tsaye daga nakasar da ya samu ta durƙushewa, tun kafin ya ruƙurƙushe ɗin bakiɗaya.

Godiya mu ke yi Hajiya Jamila.
Alhamdu Lillah! Ni ma na gode Asas.