Ba abinda ke wahalar da baƙi a Turai kamar rashin iya turanci – Amina Ahmed Gumel

“Ilimin manya makami ne na gyara al’umma”

Daga ABUBAKAR M. TAHIR

Amina Ahmed Sani Gumel ‘yar Nijeriya ce wanda ta ke zaune a Ƙasar England inda ta ke koyar da ilimin manya masu koyon yaren Turanci a matsayin yare na biyu. A cikin tattaunawarta da wakilin manhaja, ta kawo irin hanyoyin da suke bi wajen koyar da mutane baƙi yaren Turanci wanda zama ya kama su a Ƙasar England. Haka kuma ta kawo irin ƙalubalen da ta fuskanta wajen yaren Turanci dama irin nasarorin da ta samu a matsayin mai koyar da yaren Turanci a Ƙasar England. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatun mu.

HAJIYA AMINA: Assalamu alaikum. Ni dai sunana Amina Ahmed Sani Gumel, an haifeni a garin Gumel da ke Jihar Jigawa. Na taso a garin Gumel inda na yi makarantar firamare bayan kammalawa mun koma Kano inda na yi makarantar sakandare ta WAT da ke Gwauron Dutse. Bayan kammala sakandare na sake dawowa Gumel inda na shiga makarantar koyar da malamai ta ATC inda na karanci ‘Business Education’.

Bayan kammala NCE na samu aikin koyarwa a wata firamare anan garin namu na Gumel. Bayan da maigidana ya samu damar tafiya qarin karatu a nan England sai ya zama muka taho tare inda na ci gaba da karatu har na samu shaidar karatu daban-daban kamar HNd Business Studies And Accounting sai kuma na yi BA shima akan Accounting.

To da yake Turai ba kamar ƙasarmu ba ce, bazan iya aiki a banki ba tunda ina da yara sai ya zama na koma ɓangaren koyarwa tunda dama tun a Nijeriya na samu shaidar koyarwa. inda na yi PGEC akan koyar da turanci ga waɗanda suke baƙi.

Bayan na kammala na samu damar koyarwa a kwalejin ilimi da jami’o’i inda na sake komawa na yi digiri na biyu akan koyar da turanci ga baƙi.

Yanzu haka na samu ‘Certificate’ akan koyar da mutane masu shigowa domin ƙarin karatu yi masu jarrabawa. Haka kuma Ina cikin masu nema wa baƙi masu shigowa ƙarin karatu da kula da su tare da taimaka musu.

Menene ake kira da shi kansa ilimin manya?

To idan aka ce ilimin manya yana nufin ilimi ne mai dogon zango wanda ya ƙunshi mutane da suka fara daga shekaru 18 zuwa sama, wanda kuma ya zama zai ɗauki tsawon lokaci kafin a gama. Karatun da idan yaro ne zai gama shi a ƙanƙanin lokaci, amma saboda rashin cikakken lokaci zai zama dole sai a hankali ake yin sa.

ilimin manya kusan mutumin ne da kansa zai jagoranci kansa wajen karatun, Ina nufin shine zai tsara lokacin da yake ga zai iya yi dama yin sa a lokacin da ya ga yana da dama. Ilimin manya a kimiya mun ɗauke shi a matsayin makami wanda zai taimaka wajen samar da al’umma ta gari wajen ba wa al’umma dama su tsara rayuwar gabaɗaya. Wannan zai saka su samu damar gudanar da komai nasu ba tare da wani ya shiga wajen tallafa masu ba.

Misali ka ɗauka anan Turai, za ka ga mutanenmu suna shan wahala wajen rayuwa sakamakon rashin ilimin turanci, dole idan mutum zai je cefane, asibiti, kasuwa dole sai da turanci. Wannan tasa dole sai dai ka ga mutanen mu suna ɗaukan wanda zai musu tafinta daga yarensu zuwa turanci, kaga wannan zai zama baka da sirri kamar ka je gun likita dole wani ne zai faɗa masa ga abinda ke damun ka, ko da kana fama da wani abu wanda yake buƙata sirri.

Da yake kina koyar da turanci ga baƙi. Ya ki ke ganin tasirin da yaren yake da shi ga masu shiga ƙasashen ƙetare?

To a gaskiya wannan ba ƙaramar matsala ba ce, yawanci rashin turanci yakan taka wa mutanen mu birki wanda suka samu kansu a Turai , za ka ga rashin turanci ya jawo ma mutum wata matsala da zai ɗauki tsawon shekaru kafin ya warware ta.

Za ka ga wani lokacin mutanen mu suna fama da rashin gane karatu dama na ce maka ilimin manya yakan ɗauki tsawon lokaci kafin a gama shi, wannan kansa wani lokacin mutanen mu kan sha wahala wajen koyan turanci. Dsma kuma duk wanda ya karanci koyarwa ya san akwai bambanci halitta da Allah ya yi ma kowa.

Za ka ga wasu sun fi so ka nuna musu da hannu yadda za su gane, wasu dole sai ka nuna musu hoto sannan za su gane, wasu dole sai ka rubuta musu sannan zasu gane. Shine ya sa za ka ga babu style takamaiman da ake koyarwa da shi, kowane malami yana amfani da hanyar da yake ganin yawancin ɗalibain sa suke ganewa. Wasu sun fi so ka ba su da hannunsu su gwada.

To kaga koyar da shi yana da tasiri sosai wajen rayuwa a ƙasashe kamar Turai. za ka ga koda su Turawa idan kana koyar da su zaka kusan iri ɗaya ne da namu baƙaƙen bai wuce bambanci dake akwai ba na su dama yarensu ne na mahaifiya wannan kusan shine yake bambanta mu da su.

Haka kuma anan za ka ga su suna da tsarin cewa duk wanda ya shigo dole ne ya koma ya yi karatu ba za su baka gida suna ciyar da kai ba ka komai, dole ne sai ka je ka koya don haka gwamnatin zata biya kuɗi musamman ta ɗauki mutane waɗanda za su koyar da su ilimin turanci. Saboda su suna da tsarin na duk wanda yake aiki akwai wani haraji da yake bama gwamnatin wanda da shine ta ke ɗaukan nauyin al’ummarsu marasa ƙarfi.

Don haka dole gwamnatin ƙasar ta saka ya zame maka dole sai ka je ka koyi yaransu wajen ciyar da ƙasarsu gaba. Kaga wannan ya saɓa da irin ƙasashen mu ba a kula da ilimin mutane ballantana ya zama wani abu da za a ɗaukan nauyi karatunsa har ma ya zama yana aiki ana samun haraji daga gun sa.

So da a ce ƙasashe kamar Nijeriya za ta ɗauki irin wannan tsarin na bama mutane manya wanda shekarun su suka wuce 18 su rinqa shiga makarantun yaƙi da jahilci za ka ga an samu tafiyar ƙaranci ilimin manya da muke fama da shi wanda hakan zai taimaka wajen kashe rashi aiki yi da zaman kashe wando a ƙasarmu.

Waɗanne ƙalubale kibka fuskanta a ƙashin kanki a matsayin mai koyar da turanci a Ƙasar Ingila?

To a gaskiya babban ƙalubalen da na fuskanta anan shine, yanayin tarbiyyar yara kaga mu Musulmai ne bama wasa da tarbiyya irin ta Musulunci, wannan tasa na ƙi yin aikin banki ka ga a banki ba ka da lokaci iyalanka tare da ba su ilimin addini wannan tasa dole na koma ɓangaren koyarwa inda duk lokacin da ake hutun ɗalibai ni ma Ina hutu, Ina kuma kula da karatun yaran namu.

Haka kuma qalubale na biyu shine, kaga ni na zo a matsayin mai ilimi wanda nasan turanci, amma tunda da maigidana muka zo sai ya zama a jikin Visa ta babu damar yin aiki wannan ya sakani cikin wani hali amma daga ƙarshe wannan ya wuce.

Haka kuma wani ƙalubalen da na fuskan shine, mu acan za a baka kayan karatu ka je ka karanta ka yi jarrabawa ta kuma ci, amma anan sai fa ka yi da gaske za a koya muku komai ne yadda yake a baku komai na aiki ku rubuta aka dole sai ƙwaƙwalwa ka ta yi aiki wajen samar da wani abu, to kaga babu damar yin abu ba da gaske ba to gaskiya wannan tsarin ya wahalar dani amma daga ƙarshe shima an wuce gun sa.

Waɗanne nasarori ki ka samu?

To, alhamdu lillah, gaskiya an samu nasarori kamar damar koyarwa a jami’a da kwalejin ilimi ina koyar da turanci a matsayina ta baƙar bata, to kaga wannan ba ƙaramin abu ba ne. Haka kuma na samu damar ci gaba da karatu kusan kowane lokaci duk inda naga wani abu da aka ce koyar da ilimi ne za ka ga ina kan gaba wajen samun damar wannan ilimi. Haka kuma Ina karatun addini karka tsaya a guri ɗaya ka nemi duniya ka kuma nemi lahira.

Wacce shawara ki ke da ita ga gwamnatin Najeriya wajen inganta ɓangaren ilimin?

To a gaskiya Ina da kira musamman ga shuwagabannin mu wajen ganin an inganta ɓangaren ilimi domin samar da cigaba mai ɗorewa, haka kuma ina da buri ace gwamnatin ƙasarmu za ta yi amfani da dama da muke da ita wajen nemo mu mu zo mu bada gudunmawar mu a janibin ilimi wanda haka zai taimaka wajen ƙarancin ilimi da muke fama da shi.

Mun gode.

Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *