Ba Allah ne ya jefa Nijeriya halin da ta shiga ba – Obasanjo

Daga UMAR M. GOMBE, a Abuja

A cin wani saqon da ya aike na shiga sabuwar shekara, Tsohon Shugaban Qasa, Olusegun Obasanjo, ya qalubalanci Shugaban Qasa, Muhammadu Buhari da sauran shugabanni da su daina dora alhakin halin da Nijeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

Obasanjo ya bayyana haka ne a dakin karatun sa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta a Jihar Ogun a wani saqonsa barka da sabuwar shekara da ya saba aikewa a duk qarshen shekara.

Tsohon shugaban qasan ya nuna qin amincewar sa cewa, Allah ne Ya qaddara halin talauci da Nijeriya ke fama da shi, inda ya dora alhakin hakan ga shugabannin da cewa su ne suka jefa ta cikin wannan mayuwacin halin.

“Bai kamata mu riqa dorawa Allah laifin halin da qasar mu ke ciki ba, dole mu zargi kan mu. Bai kamata Nijeriya ta zama talakar qasa ba, bai kamata dan Nijeriya ya kwanta da yunwa ba.”

“Halin da muke ciki a halin yanzu zabi ne na shugabanni da mabiya. Addu’a ta ita ce Ubangiji Ya sa shekarar 2021 ta zame ma na alheri ga kowa, amma haka ba zai faru ba sai mun hada da aiki tuquru.”

Sannan sai ya sake jaddada buqatar sa ga ’yan Nijeriya cewa matuqar su na son tabbatar Nijeriyar da suke so, to wajibi ne su tashi aiki tuquru sannan su hada da addu’a, don tunkarar qalubalen dake gaba.