Ba Buhari Jihar Ogun ta Turawa kudi ba – Garba Shehu

Mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Malam Garba Shehu ya karyata zargin da wata kafar yada labarai ta buga, wai gwamnatin jihar Ogun ta turawa shugaba Buhari zunzurutun kudi har Naira Miliyan Goma Sha biyu da rabi N12,5000,000. Mai magana da yawun shugaban ya bayyana cewa, wannan magana dai kawai ta zo mu ji ta ne, babu wani kamshin gaskiya a maganar.

Malam Garba Shehu wanda shine kakakin shugaban kasar yace “Ana yada takardun ne kawai dan a bata wa shugaba Buhari suna”.

Ya kara da cewa “Rukunin gidajen da aka sanya wa suna PMB Housing Estate, bashi da wata alaka da shugaban kasa, domin gwamnatin jihar Ogun ce ta gina abinta, kuma ta sanya masa sunan shugaba Buhari domin ta karrama shi, sannan ta gayyace shi ya bude rukunin gidajen”

A cewarsa, dan gwamnatin jiha ta gina abu, kuma ta sanya sunan wani domin ta karrama shi, wannan ba ya nufin kuma abinda aka gina ya zama nasa” Kawai ana yada wannan magana ne, domin bata suna”

Shehu ya kara da cewa, kowa ya san shugaba Buhari ba barawon kudin gwannati bane, dan haka ina kira ga mutane su yi watsi da wannan labari”

Da yake cigaba da bayani, Shehu ya kara da cewa ” Kafin shugaba Buhari ya zama shugaban kasa na farar hula, dan fansho ne, kuma bai taba rajistar wani kamfani ba, balle har a bashi aikin gini a matsayin dan kwangila”

“mun yi magana da jami’in da ya sanya wannan takardu a shafin sadarwa na Twitter, kuma ya tabbatar mana da cewa, ba shugaba Buhari aka aikawa da wannan kudi ba. Hasali ma shi wanda ya sanya takardun, jami’i ne na gwamnatin jihar, ya kuma tabbatar mana da cewa, yan kwangilar da suka gina rukunin gidajen aka aikawa da kudin, ba shugaba Buhari ba. In ji shi Malam Garba Shehu

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*