Ba Buhari ne kaɗai zai kashe ilmi ba, shi Atiku murus zai masa

Daga IBRAHIM MUSA

Ga dai wani sharhi daga likitan siyasa Dakta Ibrahim Musa. Asha karatu lafiya!

Yanzu tunda ASUU ta dawo daga yajin aiki, ya kamata ta mayar da hankali wajen tattauna manufofin ‘yan takara da yadda hakan zai yi tasiri ga ɗorewa ko rugujewar ƙungiyar.

Za mu fara da Alareni Atiku Abubakar wanda ya bayyana manufarsa a kan makomar Jami’o’in gwamnatin tarayya. Shi dai Atiku ya ce zai miƙa ɗawainiya da ikon tafiyar da duk jamioi, kwlejin ilmi da makarantun ilmin fasaha ga gwamnonin kowacce jaha su ci gaba da kula da su. A tsarinsa, zai cire hannun gwamnatin tarayya ɗungurugun daga kula da harkar ilmi. Me kuke ganin zai faru ga makomar ASUU idan hakan ta tabbata?

Bari na ɗan kawo misali yadda abin yake. Jigawa na da jami’a mallakin gwamnatin jaha. Sannan akwai guda biyu, mallakin gwamnatin tarayya, banda kolejojin ilmi da kuma ɓangaren fasaha. Duk waɗannan za su dawo gwamnatin jaha ce za ta riqa kula da su daga lalitarta. Kai har asibitoci duk Atiku ya ce, jahohi zai dawo wa da ikon tafiyar da su.

A cikin manufar mulki Atiku akwai kuma batun “resource control/fiscal federalism” wanda zai bawa jahohi mallakin ma’adanai da suke da shi. Misali, jahohi masu man fetur zas u samu mallakin abinsu gabaɗaya sai dai su rika tsakura wa Gwamnatin Tarayya wani abu da za ta cigaba da gudanar da al’amuran da suka shafi tarayya. Su ma waɗanda suka shafi tarayyar ya ce zai ba wa jahohi ikon kula da yan sandansu (state police).

Wannan zai sa ‘yan kuɗaɗen da ake raba wa jahohi daga ambulan din FAAC su zamo qalilan tunda an koma tsarin kowa yai ta kansa. A irin wannan yanayin, ta yaya Jigawa ko Yobe za su iya ɗaukar qarin nauyin duk waɗannan makarantun tarayya da gwamnatin Atiku za ta dawo musu da su?

Ba mamaki jahohin su rufe makarantun tunda a yanzu ma da suke samun kuɗaɗen ba su iya kula da makarantun da suke ƙarƙashin ikonsu sosai ba. Shi tsarin jari hujja zalla yana da daɗin faɗa a baki, amma fa jama’a za su ɗanɗana kuɗarsu. Idan Allah ya bamu rai da lafiya za ku ce ni Alaramma Ibrahim Musa, na gaya muku, ba kuma duba nake ba. Kaf Nijeriya idan ka cire jahohi masu man fetur, jahar Lagos ce kawai nake ganin za ta iya tsayuwa da kanta ba tare da ambulan din FAAC ba.

Waɗannan tsare-tsare da ƙudire-ƙudire na Alereni suna iya ta’azzara matsalolin tsaro saboda za su ƙara yawan rashin aikin yi. Za su talauta milyoyin mutane da tsakar rana.

Shi ya sa ya kamata mu tattauna batun nan gwari-gwari. Shi zancen gaskiya a yi shi da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *