Ba don Shugaba Buhari ya kai ɗauki ba da tuni ‘yan bindiga sun mamaye Imo – Gwamna Uzodinma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya bayyana cewa ba don Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gaggawar kai ɗaukin tsaro a jihar ba, da tuni ‘yan bindiga da waɗanda ya kira ‘yan iskan gari sun mamaye jiharsa.

Uzodinma ya yi wannan bayani a lokacin da Buhari ke buɗe titi falan-biyu wanda ya tashi daga Owerri zuwa Orlu a ranar Laraba.

Gwamnan ya gode wa Buhari wanda ya ce shugaba ne mai ƙaunar al’ummar Igbo, musamman jihar Benuwai.

Ya ce babu abin da zai ce wa Buhari sai godiya, domin a cikin shekarar ban ya kai ziyara jihar sau biyu.

“Tun bayan yaƙin Basasa ba a yi shugaba guda ɗaya wanda ya yi aiki ɗaya na kwatankwacin maƙudan kuɗi har Naira biliyan 360 ba, sai Buhari.”

Uzodinma na magana ne kan aikin Gadar Kogin Neja wadda Gwamnantin Buhari ke aikin ginawa, gadar da ta haɗa Arewacin Nijeriya da Kudu maso Gabas.

Ya ce, “Buhari ya yi aikin ƙwarai da nuna kishi. Ba don ya yi gaggawar kai ɗaukin tsaro a Imo ba, da yanzu ‘yan bindiga da ‘yan iska sun mamaye jihar.”

Manhaja ta buga labarin cewa dattawan Ƙabilar Igbo za su sake bijiro da neman a saki Nnamdi Kanu don a zauna lafiya a yankin, yayin zaman su da Buhari a Imo.

A ranar Talata ce Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka Owerri, domin ziyarar buɗe wasu ayyukan raya jiha da Gwamna Hope Uzodinma ya aiwatar.

Buhari ya isa Jihar Imo wajen 11:30 na safe, inda Gwamna da wasu manyan jihar su ka tare shi a filin jirgi.

Cikin ayyukan da ya ƙaddamar har da titi mai hannu biyu, mai tsawon kilomita 36, wanda ya tashi da Owerri zuwa Orlu da kuma wani irin sa mai tsawon kilomita 50 da ya tashi daga Owerri zuwa Okigwe.

Daidai rubuta wannan labari Shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da manyan dattawan Ƙabilar Igbo a Owerri, inda ake sa ran za su tattauna batutuwa da dama waɗanda su ka shafi yankin Kudu maso Gabas.

Daga cikin abin da za su tattauna, ana sa ran akwai matsalar tsaron da ta addabi yankin, ciki har da jihar Imo, inda fanɗararrun IPOB ke kai wa jami’an tsaro hare-hare.

Sannan kuma ba za a rasa sake tattauna batun neman da za su sake ba, na a saki Nnamdi Kanu, wanda tsare shi da aka yi ne musabbabin tashe-tashen hankula a yankin.

A cikin watan Nuwamba 2021, Dattawan Ƙabilar Igbo sun tura wakilai wurin Buhari, domin neman a saki Kanu.

Da farko Buhari ya ce zai yi tunani kuma ya duba ya gani. Amma kuma daga baya sai ya ce ba zai tsoma baki a lamarin da ke gaban kotu ba.