Ba gaskiya ba ne zargin da El-Rufai ya yi wa Uba Sani kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi – ALGON

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kungiyar Shugabannin ƙananan Hukumomi reshen jihar Kaduna (ALGON) ta ƙaryata zargin da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufai, ya yi kan satar kuɗin ƙananan hukumomi da ya ce ana yi a jihar.

ALGON ta ce zargin da ya yi yunƙuri ne na baular da hankalin al’umma da haifar da tsana da cin zarafi da cin fuskar gwamnatin Kaduna.

A kwanakin nan ne El-Rufai ya zargi cewa gwamna Uba Sani na karkatar da kuɗin ƙananan hukumomi tare da sayen kadarori da Seychelles da Afirka ta Kudu da Ingila.

A yayin da yake tsokaci kan wannan batu ga manema labarai, mai magana da yawun ALGON, Alhaji Muhammad Lawal Shehu, ya ce, gwamnatin Uba Sani mai bin doka da oda ce yadda ya kamata.

Ya ce gwamnatin Kaduna tana yin komai nata ne a buɗe tare da girmama dokar bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin kashe kuɗaɗensu. Sannan gwamnatin ba ta taɓa yin katsalandan ba ga harkokin ƙananan hukumomi.

Saɓanin abin da El-Rufai ya faɗa, ya ce, gwamnatin Uba Sani na ɗaukar dukkan matakai da ayyuka domin tallafa wa ƙananan hukumomin.

Alhaji Muhammad ya ce, ga mafi yawa daga cikinsu da suka yi zamani da Mal. Nasir el-Rufai a matsayin shugabannin ƙananan hukumomi, a yanzu suna karɓar ninki biyu ne na abin da suke samu a da.

“Baya ga samun kuɗinmu duk wata, yanzu mun rabu da cuzgunawa da barazana da aka sha fama da ita a lokacin mulkin El-Rufai,” ya faɗa.

Ya ce a lokacin mulkin tsohuwar gwamnati, Malam Nasir El-Rufai ya ƙirƙiri wani tsari na zabtare kuɗi da sunan ‘kuɗin diyya’ musamman ga ƙananan hukumomin da ke Kudancin Kaduna.

“Wani tsari ne na ladabtarwa ga mutanen Kudancin Kaduna na ƙin mara wa gwamnatinsa baya. Wannan mummunan tsari ya haifar da rarrabuwar kai da faɗace-faɗace na kabilanci a jihar. Amma alhamdulillah, yanzu an sauya wannan tsari da zuwan gwamnatin Uba Sani.”

A cewar Alhaji Muhammad, ‘shirin raya karkara da gwamnatin Uba Sani ta kawo na taka rawa wajen inganta tattalin arziƙin mutanen karkara da ba su sabuwar rayuwa.

“An buɗe inda yankunan da ba a iya shiga, an farfaɗo da aikin gona, an samar da ayyukan yi kuma an dawo da zaman lafiya da tsaro.”

Kakakin na ALGON ya ce wannan ƙungiya tasu, “tana sa ran mutum kamar Mal. Nasir El-Rufai zai riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin ya faɗe su a bainar jama’a. shugabannin ƙananan hukumomi 23 na Kaduna suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.”

“Mun ƙagu mu ga mun magance matsalolin da ke damun al’ummarmu. Muna jin daɗin irin ƙarfin guiwar da goyon bayan da muke samu daga gwamnatin Uba Sani. Ba mu taɓa samun wani dalili da zai tilasta mana mu yi ƙorafi ba,” ya faɗa.

Daga ƙarshe, kakakin ya shawarci al’umma da su yi watsi da dukkan abin da Mal. Nasir El-Rufai ya faɗa, saboda zargi ne marar tushe.