Ba jihohi biyar kawai ke muna-munar jarrabawa a Nijeriya ba – Ƙungiyar NAPPS

Daga Muhammadu Mujitaba

Shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar Makarantu masu zaman kansu a Nijeirya (NAPPS), Dakta Sa’idu I Mijinyawa, ya bayyana cewa, babu wani abu da zai kawar da matsalar maguɗin jarabawa sai duk masu ruwa da tsaki sun tashi tsaye wajen ganin an ji tsoron Allah ta hanyar gyara ilimi a kowa ne mataki na karatu musamman ganin yadda ake koka da yawaita maguɗin jarabawan da ya zama ruwan dare a Nijeriya wanda kuma ya wuce ace an ware wasu Jihohi biyar a arewa da aka ce su ne kan gaba wannan ne dai ban yarda  ban gamsu ba domin amin ya yi kama da maganar siyasa kon san rai.

Dakta Sa’idu ya bayyana hakan ne a lokacin ya ke magana da ‘yan jaridu a Kano.

Dakta I Mijinyawa ya ce, yasan yadda aka yi karatu a shekarun baya yanzu abun ba haka yake ba don haka akwai buƙatar iyayen yara da ɗaukacin al’umma a tashi tsaye wajen gyaran ilimi a matakan jihohi da ƙasa baki ɗaya ba, wai a cigaba da zargin wasu Jijoji a arewa ba cewa sune kankaba wajen maguɗin jarabawa wannan ta yi kama da maganar siyasa ko san rai a wannan lokaci.

Har ila yau, shugaban kwamitin amittatun na ƙungiyar ‘yan NAPPS ya ce, maguɗin jarabawa rashin tarbiya ne rashin tsayuwane ga hukumomin ilimi domin babu wata ƙasa ko al’umma da zata cigaba da maguɗin jarabawa domin matsala ce da take samun al’ummar Nijeriya masu kishin ilimi masu kishin ƙasarsu mu a NAPPS muna da tsari na yaƙar maguɗin jarabawa domin matsala ce a ilimi matsalace a rayuwa burinmu mu ba da ilimi da tarbiya domin samun shugabanni na gari a Nijeriya.

A ƙarshe ya yi kira ga hukumomin ilimi a matakan tarayya da Jihohi su inganta ilimi kamar yadda ta yakamata su kuma makarantu masu zaman kansu su maida hankali wajan tarbiya da ilimi kamar yadda suka yiwa iyayan yaro alƙawari na riƙon amana domin cigaban Nijeriya domin ko nawa aka biyaka ka yi taimako ga hukumomin Nijeriya ta hanyar ragewa Gwamnati nauyi da kuma ɗaukar ma’aikata masu koyarwa a makarantun mu da sauran ma’aikatanmu kuma aji tsoron Allah a dukkan lamari na rayuwa.