Ba kare bin damo: Rundunar soja ta kammala biyan haƙƙin tsoffin sojoji

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar sojojin Nijeriya ta biya dukkan haƙƙoƙin tsofaffin jami’anta da kuma na magadan sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki. 

Hukumar kula da fanshon sojoji (MPB) ta kammala biyan ƙarin mafi ƙarancin albashi da kuma basussukan albashi ga tsaffin ma’aikatan da suka cancanta, wanda aka fara tun ranar 6 ga Mayu, 2022, wanda aka kammala a ranar 10 ga Mayu, 2022.

Hakazalika, hukumar ta iya dukkan iyalan mamatan sojojin waɗanda suke bin bashin haƙƙoƙinsu su ma an biya su, ba sa bin ko sisi. 

Don haka, hukumar fanshon sojojin ta cika alƙawuran da ta ɗaukar wa dubban sojoji na cewa za ta biya su haƙƙoƙinsu da zarar gwamnatin Tarayya ta sakar musu kuɗaɗen.

Shugaban hukumar fanshon sojojin,  Rear Admiral Saburi Abayomi Lawal shi ya tabbatar da wannan jawabi a wata takarda mai dauke da sa hannunsa. Inda ya bayyana cewa,  tabbas an sanya kuɗaɗen a cikin asusun bankuna ‘yan fanshon da suka cancanta. Don haka dukkan Waɗanda suke da haƙƙi da su garzaya bankunansu don amsar haƙƙoƙin nasu. 

Lawan ya ƙara da cewa, wannan shi ne rukuni na biyu da hukumar ta biya. Bayan ta cimma yarjejeniya da Ma’aikatar kuɗin da Kasafi ta tarayya ta saki kuɗin.   

Lawan ya ƙara da cewa, “Yana da muhimmanci a san cewa, wannan biyan kuɗin da ake yi bashin albashi ne wanda ƙari ne na albashi da aka yi wa ‘yan fanshon bayan an sanya dokar ma fi ƙarancin albashi ga sojojin masu ritaya bayan garambawul ga dokar albashi a 2019. Waɗannan sojojin da aka biya, su ne Waɗanda aka sanya sunayensu a jadawalin biyan albashin tun a 18 ga watan Afrilun, 2019 zuwa 30 ga Afrilun 2022” 

Daga nan ya gode wa Gwamnatin tarayya a kan irin gudunmawar da ta bai wa hukumar tasu. Domin a cewar sa, ba don goyon bayan da suka samu daga gare ta ba, da ba su samu irin nasarar da suka samu wajen gudanar da aikin biyan haƙƙoƙin ba. 

Sannan kuma ya gode wa Shugaba Muhammad Buhari, da kuma Ministan tsaro, Manjo Janar BS Magashi (Mai ritaya) da sauran muƙarrabansa saboda gudunmawa da goyon bayansu. Sannan har ma da al’ummar Nijeriya masu yi musu fatan alkhairi. 

Idan ba a manta ba, hukumar ta fara biyan rukuni na farko na tsaffin ma’aikatan tsarin tun a watan Fabrairun shekarar nan ta 2022. Inda a wancan lokaci sama da tsofaffin sojoji da iyalan marigayan sojoji dubu casa’in ne aka ba kaso 25 na bashin ƙarin albashin.