Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shiga mawuyacin hali kan tsare ƙananan yara masu zanga-zangar tsadar rayuwa guda 76.
An ruwaito cewa a ranar Juma’a ne aka gurfanar da yaran a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, inda huɗu daga cikin su suka yanki jiki yayin da ake tsaka da shari’ar.
Da farko dai, Sufeton ƴan sanda ya shigar da mutane 11 ƙara a gaban Alƙali Emeka Nwite kan zargin hamɓarar da gwamnati da cin amanar ƙasa waɗanda laifuka ne da suka saɓa wa dokar ƙasa sashi na 97.
An kama masu zanga-zangar ne a rana ta 10 a Jihohin Abuja, Kano, Kaduna, Katsina Sakkwato da Gombe yayin da aka samu tashe-tashen hankula da kashe-kashe a wasu sassan Nijeriya.
A yayin shari’ar ne, Mai Shari’a Oboira Egwuatu ya yanke Naira miliyan 10 a matsayin kuɗin belin kowane ɗaya daga cikin matasa 67 ciki 76 da aka gurfanar.
A lokacin da ya ke magana game da batun, tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Tinubu kan kamawa da tsare masu zanga-zanga 76 da aka yi.
Ya nuna damuwa kan bidiyon ya karaɗe kafafen sadarwa da ke nuna yaran a hali na rashin samun isasshen abinci a lokacin da aka gurfanar da su, ya na mai cewa wajibi ne a kare ƴancin yara da mutuncinsu, kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar.
Ya kuma soki tsare yaran da aka yi na tsawon lokacin watanni uku kafin gurfanar da su a kotu, waɗanda suka nuna rashin jin daɗinsu ga tsauraran matakai da gwamnati ke ɗauki da suka haifar da tsadar rayuwa.
Haka ma, tsohon Ministan Ilimi, Oby Ezekwesili ya rubuta buɗaɗɗiyar wasika zuwa ga shugaba Tinubu kan ya umarci a gaggauta dakatar da binciken marasa galihun.
Sannan, tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya aika da saƙo ga hukumar ƴan sanda kan bidiyon da ke nuna halin da yaran ke ciki inda ya ce hakan ya saɓa wa ƙa’idar zamantakewar duk wata al’umma mai karamci.