Ba laifi ko rashin so ke sa maza ƙarin aure ba – Sa’adatu Kankia 

Yana daga cikin matsalar maza wofuntar da matansu idan za su ƙara aure – Likitar Ma’aurata 

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, kuma sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja. A wannan satin kamar yadda mukan yi a wasu lokuta mun tattauna kan ɗaya daga cikin ababen da ke ci wa ma’araurata tuwo a kwarya, wato matsalolin da ke tasowa yayin ƙarin aure.

Domin kawo maku gamsashen bayani, mun gayyato maku sanannun mata da suka jima suna bayar da gudunmuwa a zamantakewar aure, wato Sa’adatu Saminu Kankia, da kuma Zuwaira Kolo, wadda ku ka fi sani da Likitar Ma’aurata. Don haka idan kun shirya, sai in ce Allah Ya sa mu amfani juna;

MANHAJA: Muna yi wa baƙinmu barka da zuwa wannan tattaunawa da shafin Gimbiya na jaridar Blueprint Manhaja.

LIKITAR MA’AURATA: Masha Allah. Muna amsawa. Assalamu alaikum.

SA’ADATU KANKIA: Masha Allah! muna godiya.

Sis Kolo bari mu fara da ke. Shin me ke sa maza ƙarin aure?

Sis Kolo: Assalamu alaikum. Zan fara da godiya sosai a bisa wannan damar da aka ba ni, ina godiya.

Abubuwa da yawa suna saka maza ƙarin aure. Ga wasu daga ciki;

1. Sha’awa.

2. Halayen wasu matan da suka aura mara daɗi.

3. Niyya kawai na ganin dama Saboda samuwar budi da arziki da damar hakan daga wasu mazan.

4. Neman zuriya da yawa.

5. Rashin gamsuwa daga mazajen.

6. Auren da aka tilasta ta gefen iyaye.

Na ɗaya daga cikin tambaya mafi karakaina a zuciyoyi da ƙwaƙwalwa musamman ta mata cewa: me ya sa namiji zai ƙara aure? Bayan yana zaune da matarsa lafiya ƙalau? Wasu kuma tsawon lokaci ake shafewa har sai an sallama da tunanin auren sai kawai a ga ya bijiro da shi.

Kamar yadda na ambata da yawan maza suna da dalilai ko sabuba da suke ƙara aure. Kuma bayan hakan akwai wani abu da ake cewa daɗi ba ya hana su kwaɗaituwa da jin son ƙari ko zaman lafiya. Kamar yadda ba abu ba ne mai sauƙi a iya dakatar da maza kan ƙara aure amma hakan ya danganta da yadda suke mabambanta a dalilai.

Misali wani namijin za ka iske babban burinsa ya zauna da mace ɗaya har abada. Amma bayan auren sai ya iske tarin wasu abubuwa da aka gaza da zai ji kawai kamar zai iya samo su a wasu wuraren. Ga misalin abubuwan;

1. Rashin kulawa da kyautatawa ko kuma girmamawa a tsakani.

2. Rashin tsafta ko gyaran gida gida ko yara da rashin alkinta duk wani abu da ya kawo wato almubazarranci.

3. Rashin samun biyan buƙatar da gamsuwa a shimfiɗa wanda hakan ya sanya ya ga da ya afka hallaka gwara ya yi auren.

4.Rashin iya girki na wasu matan, da kuma wofintar da surukai, ko kuma ‘yan uwan namiji da wulaƙanta su.

5. Neman haihuwa wanda wasu za a ga ba a samu ba matsalar ba daga gare su ba ne, ko kuma dai, son a ga an tara zuriya sosai.

Wannan suna iya janyo wa a ƙara aure, suna kuma sa wa a fasa idan su matan sun canja da abubuwan da aka rasa a tare da su

Hajiya Sa’adatu: Za mu so jin na ki ra’ayin kan dalilan da ke sa maza ƙarin aure.

Assalamu Alaikumu. Barkanmu da saduwa a cikin wannan dandaki mai farin jini. Watau akwai dalilai da dama da ke sanya maza ƙara aure, daga ciki akwai, 

Halitta, Allah {SWA) da ya halicci zuciyar namiji, bai yita don ta so mace ɗaya ba, zuciya ce mai sha’awa akan mata, ko da namiji ya zauna da mace ɗaya, dole akwai wata mace ko wasu mata da ke tasiri acikin zuciyarsu kawai dai Allah bai ƙaddara za su yi aure ba.

Akwai lalura ta rashin lafiya, ko rashin samun kulawa da sauransu. Akwai wadata, wani samun wadata ko ɗaukaka na sanyawa ya ƙara aure saboda hidimomin gida na rayuwa. Ra’ayi wani dama tun farko tsarinshi mutum ne mai sha’awar zama da mace sama da ɗaya. A hakan ya tsara rayuwarshi. Wani kuma yana ƙara aure ne saboda sunna ce ta manzo S.A.W.

Don haka ƙarin aure, yana zuwa ne a rayuwar namiji dai dai da ƙaddarar rayuwarshi. Akwai maza da yawa da ke son ƙarin auren, ko kuma ya dace su ƙara ɗin, saboda lalura daga ɓangaren macen, kazanta, rashin kyautatawa da sauransu, amma sai kiga ba su ƙara ɗin ba, saboda baya cikin ƙaddarar su, wani kuma babu abinda ya rasa, ana yi mashi biyayya kamar za a kwanta ya taka, amma sai ya ƙara, saboda hakan ƙaddarar shi ce.

Sis Kolo: Kin yi zancen matsalolin da ake samu a zama da mace zai iya zama silar ƙara aure ga namiji. Wannan dalilin ne kawai ke zuwar ma mata yayin da aka ce mazajensu za su kara aure, wato me na yi masa, ko menene ba na masa. Duk yadda za ka lurar da mace saɓanin hakan zai yi wuya ta saurare ka. Shin ko hakan na da nasaba da irin hallayar da mazan ke bijirowa da su yayin da suka fara neman auren?

Gaskiya Idan an bi ta ɓarawo a bi ta mabi sawu. Yana daga cikin babbar matsalar maza shi ne idan suka samu wata za su aura sai kuma ta gidan ta zamo abar yarwa abar wofintarwa abar nuna ita ba komai ba ce an ci moriyar ganga.

Wasu mazan sai ka ga har waya suke yi a gaban ta gida, wasu kuma su riƙa zumuɗi da sakin kuɗaɗe da hanzarin yi wa wancan duk abin da suke so. Wani ma sai ya ƙauracewa matar ta shi. Mafi muni shi ne wanda ke kwasar sirrinsu su kai wa wancan ƙarshe sai ta shigo gidan da raini da tunani ita ta gidan ba kowa ba ce. Ka ga tun anan miji ya kafa harsashi na dagula zaman lafiya na gidansa.

Wannan ya sanya matan ke jin tsoron, ke kuma tashi tsaye suna ganin wata daban za ta zo ta ƙwace komai. Kuma a sanadin ta an wulaƙantasu.

Hajiya Sa’adatu: Shin mace ta cancanci a bar ta ta yi hauka kowacce iri ce da sunan za a yi mata kishiya, tunda dai an ce kishi kumallon mata?

Idan ni namiji ce! alokacin da nike shirin ƙarin aure, zaniyi bakin ƙoƙarina wajen ganin na ba matata dama ta yi duk iya haukan da zata yi domin nuna kishinta, sai dai zaniyi bakin ƙoƙarina wajen tausar da zuciyarta, kyautata mata da nuna mata har yanzu ina sonta.

Kuma dama waɗannan abubuwan su ne abinda mace ke so ayayin da miji zaya ƙara aure, indai mai hankali ce ba mai son zuciya ba, muddin mijinta ya nuna yana tare da ita, za ki ga kishin nata da sauƙi, kuma zata yarda ta ba shi dama. Akasin yarda wasu mazan ke yi, da kansu suke tunzura matan ta hanyar wulaƙanta su, gaya masu magana da nuna masu su ɗin ba wata tsiya ba ce.Wanda wannan abin ne ke sanya wasu matan hauka, wasu kuma zafin kishin su halitta ne.

Sis Kolo: Waɗanne irin hanyoyi ki ke ganin ya kamata namiji ya bi don ganin ya yi wa ta cikin gida adalci tun kan a kawo amaryar?

Hanyoyi da yawa kam amma daga ciki akwai waɗannan;

1. ƙauracewa duk wani abu da zai taɓa martaba da ƙimar uwar gida.

2. Linka farashin kulawa sosai da kyautatawa tare da haƙuri da juriya wajen rarrashi ta ciki da gwada mata ba wai za ka yi hakan ba ne, domin wulaƙanta ta ko kuma daina son ta.

3.Kaucewa aiwatar da wasu abubuwa a gaban ta da zai taɓa zuciyar ta kamar yin waya bayan ka dawo gida, ko kuma dai yin wasu abubuwa da yawa da a da kwata kwata ba ka yi da nufin faranta wa amaryar da za ta shigo.

5. Idan ka girmama kan ka, ka kaucewa ƙananun maganganu da yada magana tsakanin gidan da waje, hakan zai sanya a samu zaman lafiya ko an shigo.

Hajiya Sa’adatu: Wasu na ganin ajiye mata kusa da juna ba tare da tazara ta miƙe ƙafa ba ne babban silar wanzuwar matsanancin kishi a tsakanin kishiyoyi. Shin menene gaskiyar wannan maganar?

Matan zamani ba, Idan akwai fahimta kuma namiji mai adalci ne, aje mata kusa da juna ba matsala ba ne, to amma yanzu daga mazan har matan babu adalci a zamantakewarsu babu amana, son zuciya sun rinjayi zukatansu, za ki ga ko an zauna ɗin miji na son ya yi adalci, uwargida zata koma gefe ta ce so take yi sai an fifita ta da amarya, sabida yau tazo, ko kuma a rinƙa gallaza mata da ƙuntata mata, wani kuma da kanshi yake wargaza zaman ta hanyar kasa yin adalci a tsakaninsu, fifita amarya ko uwargida. Don haka wasu ke ganin zaman nesa ya fi. Sai dai ga namiji jarumi wanda ya fi ƙarfin gidanshi, zaman kusa ya fi, kuma ya fi ƙara danƙon ƙauna da shaƙuwa a tsakanin iyalinshi.

Sis Kolo: Kin yi zancen ganin dama na wanzuwar arziki kan iya sa namiji sha’awar ƙara aure. To ina zancen mazan da za ki tarar ko ta ciki ba su iya riƙewa sosai ba, amma da sun ɗan samu wata ‘yar dama ta wucin gadi, sai kiga sun dame ta da ƙara wani auren. Me za ki ce kan irin waɗannan?

E akwai halitta gaskiya ta wasu masana, sannan ina yawan ba maza shawara su ƙara aure ba ina nufin su ƙara haka kawai ko ba su da hali ba ne a’a, ina nufin wanda Allah ya hore ma wa ya ƙara aure.

Sannan akwai wani ‘posting’ da na taɓa yi cewa da ina da hali da na ara wa maza kuɗi su ƙara aure. Dan haka idan na ce halitta ina nufin kawai Allah ya halicce su ne ba za su iya zama da mace ɗaya ba, ina nufin mace ɗaya baza ta iya gamsar da su ba, so za ki ga ko ta yaya ne suna ƙoƙarin ganin sai sun ƙara ko da kuwa matar gidan na yin biyayya da faranta ran maigidan.

Sannan babu shakka yana daga cikin ɗabi’u na maza hakan, wani tun farko za ki iske daman yana da buri da muradin ƙara aure. Amma rashin dama ce, irinsu ko ya suka samu dama sai ka ga sun yi aure. Ba zan ce babu kuskure ba a ciki, ko kuma ta wani fuskar rashin kuskure ba.

Amma magana da tsari na cikakken hankali da nagarta shi ne abu ne mai kyau mutum ya tsaya ya tabbata yana iya sauke duk wani haƙƙi da ya rataya a wuyansa kafin shigo da wata ƙari. Ta yiwu shi ya sanya ma ake ta ambaton adalci adalci adalci ke nan wannan kalmar ta haɗa tarin abubuwa sosai. Kuma gargaɗi ce da gugar zana da a tabbatar an yi za a yi adalci kafin auren. Idan kuma an gaza da hakan haƙuri ya fi dacewa a yi domin gujewa garin gyaran gira a rasa idanu. A ɓangaren daidai kuwa wasu za su iya yi yin auren bisa kar su je su afka ga hallaka da ta fi auren hakan. Akwai kuma wani tunani na daban da ake da shi cewa ko wacce mace da arzikinta ke shigowa me yiwuwa hakan zai sanya mutum ya ji yana so ya ƙara auren da niyyar samun yalwa na budi.

A ƙarshe ina jan hankali ga maza a nan su tsaya su yi karatun ta nutsu domin tabbatar da cewa abin da za su aiwatar don gudun afkawa cikin komar danasani. Kuma kwanjin ƙarin aure a zuciya yake, wani duk kuɗinsa za ki ga ba zai ma iya ƙarin auren ba.

Har yau dai muna kanki Sis Kolo, zancen sha’awa da ki ka yi a matsayin dalilin da ke sa maza ƙarin aure. Sau da yawa mata kan yi ƙorafin mazajensu ba su cika ɗauke masu tasu sha’awa ba yadda su suke buƙata. Kina ganin a irin hakan idan namiji ya yi aure ba zai cutar da ta ciki ba, har ma da wadda zata shigo ba, koda kuwa yana da tarin arziki?

Maganar namiji bai ɗauke sha’awar mace ba duk babu ita ko kuma ince bata cika tasiri ba, domin yawancin ma’aurata musamman mata ba su san bambancin jin daɗi wato (sha’awa) da kuma gamsuwa ba shi ya sa ake samun yawan matsaloli a zamantakewa, ki ji mace na iƙirarin mijinta ba ya gamsar da ita tunda ba ta san menene asalin gamsuwar ba. A haka za ki ga mace ta ginu a kai har ta kai ta ga cewa ita fa auren nan zaman dole take yi tunda ba a gamsar da ita har ta kai ta ga fara janye wa maigidan gabaɗaya shi kuma sai kiga ya ƙagu ya ƙara aure.

To a irin hakan za ki sha mamaki idan ya ƙara auren sai ki ji shi da amarya muƙus saboda ya samu wadda tasan kansa ta iya, kuma take bambance tsakanin sha’awa wato jin ɗaɗi da gamsuwar. 

Shi namiji komin ƙanƙantar sa, komai rashin wayewar sa ko da kuwa bai taɓa sanin wacce ce mace ba aka ɗauka aka ba shi, duk ranar da zai fara mu’amala da ita zaki sameshi ‘professor’ ne a wannan fannin. 

So kinga kenan ba lallai dan ta gida ta ce ba ta gamsuwa ake yarda da lallai hakan ba ne domin duk namijin da ki ka ga yana yawan maganar zai ƙara mata ko ya ƙara ɗin to gaskiya bai gaza ba.

Hajiya Sa’adatu me za ki ce ga matan da mazajensu sun yi irin yadda ki ka ce na ba su damar bayyana kishinsu tare da rarrashi, amma hakan bai sa suka sunkuya ko suka haƙura ba, asalima wasu kan ƙara harzuƙa ne idan ana rarashinsu, a cewarsu a bige ka ne kuma a hana ka kuka?

Shi ne na ce idan mace ba mai son zuciya ba ce, akwai matan da kishinsu son zuciya ne, saboda su kansu sun san mijinsu na son ƙara auren kuma ta kowacce siga yana da halin ƙarin kuma ya cancanta ya yi, kuma su kansu sun tashi sun ga kishiya a gidansu, amma a gidan miji sai su ce ba su yarda ayi ba. Irin waɗannan komai za a yi masu ba za su daina ba, sai dai kawai a bi su da addu’a, da kuma nasiha.

Sis Kolo, a ganin ki idan namiji ya aikata hanyoyin nan da ki ka ambata za a iya samun gushewar fitintinu daga uwargidan?

Tabbas idan ya aikata waɗannan hanyoyi za a samu gushewar fitintinu daga uwargida, sai dai idan dama sheɗaniya ce wacce bata son a zauna lafiya.

Akwai wasu sababbin ɗabi’un da mata ke bijirowa da su a yayin da aka ce miji ya ɗauri aniyyar ƙara aure, waɗanda ke iya kai wa ga yunƙurin hallaka miji ko amaryar da za a aura ko aka aura. Sis Kolo, a fahimtar ki ina wannan ɗabi’a ta samo asali ko in ce me ke kai mata ga wannan ɗanyen aikin?

E ba wani abu ke jawo hakan ba illa zallar sharrin shaiɗan, son zuciya da rashin sanin addini.

Wasu matan kuma suna ganin sun daɗe da miji tun ba shi da ko sisi, wasu ma su suka gina mijin da dukiyarsu kuma ace yanzu zai ƙaro abokiyar zama?

Wasu suna ganin abin kunya ne yanda suka amsa sunan su na mata kuma ace an musu abokiyar zama, aji da ƙimarsu zai ragu a idon aminan su da makusanta

Akwai masu ganin cewa suna da kishin da idan mijinsu yazo da maganar aure da su yarda su zauna da kishiya gwara ayi haihuwar guzuma. Imma macen ta kashe mijin, ko ta kashe ita wacce za a aura, ko ta kashe kanta. Allah ya kiyashe mu. 

Ki lura yawancin mazan da ba su da kirki basa riƙe matansu su ba su haƙƙinsu za ki ga idan suka tashi ƙara aure matan su ba su cika jin ɗar ba saboda sun san idan ma suka shigo ai ba komai zasu rage su da shi ba tunda dama zaman ragaita suke yi.