Ba mu amince da haramta wa mata saka niƙabi a Jami’ar FUNAAB ta Ogun ba – MURIC

Daga WAKILINMU

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmai (MURIC) ta nuna rashin amincewarta da hana sa niƙabi ga matan Musulmai da hukumar Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Abeokuta (FUNAAB) ta yi.

Jami’an tsaron makarantar sun tilasta wa wata mace, wacce ta kammala jami’ar cire niƙabin da ke sanye a fuskarta kafin su bar ta ta shiga harabar jami’ar.

Yayin mayar da martani akan wannan lamari, Daraktan MURIC, Malam Ishaq Akintola, a wata takardar da ya fitar cikin makon nan, ya ce, kowa ya na da damar yin shigar da addininsa kamar yadda ya yarje masa a duk jami’o’in ƙasar nan.

“Babu wata makaranta, tun daga firamare zuwa jami’a, ta jiha ko ta tarayya ko kuma mai zaman kanta da ta ke da damar hana anfani da hijabi ko niƙabi. Hakan ya ci karo da sashi na 38(i) da (ii) na kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda ya ce, ko wane mutum yana da damar amfani da fahimtarsa da addininsa, da kuma damar sauya addininsa kuma ya yi duk harkokin addinin kamar bauta, koyarwa da ayyuka,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, “har ila yau a wata takarda ta 18 ta ICCPR ta ba mutum damar yin addininsa ba tare da wani cikas ba.

Ya ci gaba da cewa, cutarwa ne sanya dokakokin da za su hana musulmai walwala ta hanyar hana su shigar da addininsu ta tanadar.

Akintola ya ce, dokar jami’ar ta ci karo da wasu sassani na kundin tsarin mulkin Nijeriya. Don haka ba zai yiwu a bi duk wata sanarwa da doka ta hana saka niƙabi da Jami’ar FUNAAB ta kafa ba a gaba ɗaya ƙasar Yarabawa.