Ba mu da masaniyar bai wa Emefiele izinin barin ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce ba ta da masaniyar izinin fita waje ƙaro ilimi da aka ce Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Babban Hadimin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Malam Garba Shehu ne ya faɗi hakan, yayin amsa tambayar jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi.

A baya, an rawaito Shehu na cewa, “Idan ma Shugaba Buhari ya bai wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, izinin fita ƙaro ilimi, ba mu san da haka ba.

“Haka nan, sakatariyar Shugaban Ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, ba ta san da haka ba.”

Kwanan nan jaridar SaharaReporters ta rawaito cewa, Buhari ya bai wa Gwamnan CBN izinin fita ƙetare don ƙaro gabanin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, wanda zai gudana ran 29 ga Mayu.

Jaridar ta ƙara da cewa, bai wa Emefiele izinin barin ƙasar na zuwa ne daidai lokacin da ake zargin Gwamnan CBN ɗin da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *