Ba mu da matsalar albashi ko ƙarin girma ƙarƙashin Ganduje – Shugaban Ƙungiyar Malamai

DAGA MUHAMMADU MUJITABA

Shugaban Ƙungiyar Malaman Sakandire ta Ƙasa reshen Jihar Kano (ASUSS), Kwamared Abdu Usman Yalo ya ce su malaman sakandire na Jihar Kano ba su da matsalar biyan albashi daga gwamnatin Kano ko matsalar rashin ƙarin girma, ya ce  duk wata ana biyan su albashi tun tsohuwar gwamnati har zuwa gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ba su da matsalar rashin biyan albashi kamar yadda wasu jihohin ƙasar nan ke fuskantar matsala.

Usman ya ƙara da cewa “ƙarin girma shi ma ba mu da matsala ana yi kamar yadda ya ke  a ƙa`ida sau biyu a shekara, ana mana kan wannan sai mu godewa Ubangiji kuma  mu riƙe amanar da aka ɗora mana kamar yadda ya kamata da kuma bai wa gwamnati haɗin kai.”

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai  a birnin Kano a ranar Litinin da ta gabata.

Har ila yau ya ce duk da yake wannan ƙungiya ta su jaririya ce in ka kwatantata da sauran ƙungiyoyi, amma yanzu haka tana da mambobi sama da dubu ashirin a Kano kawai. Kuma suna bada gudunmawa wajen cigaban ilimi a Kano da ƙasa baki ɗaya.

Wajen ci gaban ilimi kuma suna da fahimta ko raayin cewa yajin aiki bai tava zama mafita ta ƙarshe ba, don haka su basu taɓa shiga yajin aiki ba, ya ce akwai ma lokacin da aka shiga wani yajin aiki sai su ka ga jarrabawa ta zo su suka ƙi shiga yajin aikin, saboda su taimaka wa ɗaliban su don rubuta jarrabawar su bisa laakari da cewa sun ga makarantu masu zaman kansu na zuwa makaranta kuma ba a hana su jarabawar ba, su ma su ka sa mu fahimtar juna a tsakanin su da sauran masu ruwa da tsaki a kan wannan lamari, suka ci gaba da zuwa makaranta har aka kammala jarrabawar a wannan lokaci.

Haka kuma ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga gwamnatin Kano kan ta tallafa musu wajen wadata makarantun sakandire da kujerun zama da sauran kayan aiki don amfanin malamai da ɗalibai musamman bisa la`akari da kyakkyawar manufar gwamnatin Dr. Ganduje na ilimi kyauta kuma dole a wannan lokaci.

A ƙarshe ya ce  yanzu matsalar su kawai a ASUSS ita ce rashin ofishin ƙungiya, inda ya ce wannan babbar matsala ce da ƙungiyar su take fuskanta, sai kuma matsalar rashin abun hawa wanda tun tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011 da gwamnati ta ba su mota har yanzu ba su samu wata ba, don haka suna neman gudunmawar duk wani mai kishin ilimi da al`umma kan wannan matsala ta su.