Ba mu da tabbacin za a gudanar da Hajjin 2021 – NAHCON

Daga AISHA ASAS

Hukumar Alhazan ta Nijeriya (NAHCON) ta ce kawo yanzu ba ta tabbacin ko za a gudanar da aikin hajjin bana, amma cewa tana kyautata zaton yiwuwar hakan.

Bayan taron liyafar karrama sabon Jakadan Saudiyya a Nijeriya, Faisal bin Ibrahim Al-Ghamdi, NAHCON ta ce ba a kai ga sanya hannu na yarjejeniyar gudanar da aikin hajjin ba kamar yadda aka saba amma hukumar a shirye take don fara aiki da zarar ta samu amincewa daga Gwamnatin Saudiyya.

Hukumar ta ce dare da rana tana kan tsare-tsare na zaman ko-ta-kwana kan izinin gudanar da aikin da Hajji wanda hakan bai samu a bara sakamakon Saudiyya ba ta buɗe ƙofa ga maniyyatan ƙetare su shigo ba a bisa dalilin annobar korona.

Jami’ar Labarun Hukumar Fatima Sanda Usara ta ce an yi sa’a Saudiyya ba ta sanya Nijeriya a jerin ƙasashe masu tsananin ƙalubalen korona ba, da ke nuna matuƙar za a bada dama wata ƙasa ta taho da alhazanta, Nijeriya za ta samu tagomashi.

A nasa ɓangaren, Shugaban Kwamitin Harkokin Ƙetare na na Majalisar Dattawa, Adamu Bulkacuwa, ya ce batun zuwa hajjin bana na nan bisa fatan alheri da a ke yi.