Ba mu gamsu da rawar kafafen yaɗa labarai ba – Tsohon minista Shamsudden

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Ƙungiyar ƙwararru ta Kano da Jigawa, wato Kano Jigawa Professional Forum (KJPF), ta gudanar da taron tattauna musayar Ilimi da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai, da ya gudana a ɗakin taro na Makarantar Nazarin Harkokin Kasuwanci ta Dangote da ke Jami’ar Bayero a Kano ranar Asabar da ta gabata.

Taron ƙungiyar da Kuliya A. Zubair ke a matsayin Daraktanta, taken taron dai shi ne “Zuba Jari da Bunƙasa Kafafen Yaɗa Labarai”, ya samu halartar mamallaka kafafen yaɗa labarai da dama da ke cikin jahohi.

Tun da farko a jawabinsa, tsohon ministan tsare-tsare, Dr. Shamsudeen Usman kuma shugaban ƙungiyar ya ce maƙasudin shirya taron shi ne kishin ƙasa da kuma kishin jahohi nan guda biyu.

Inda ya ce, “Idan kuka duba jihohi nan su suka biya kuɗin makarantarmu, kamar ni ka ga har zuwa Digiri na uku jihar Kano ce ta biya min, shi yasa za ka ga mafi duk membobin ƙungiyar duk ƙwararru ne wanda kowanne za ka ga sai da ya riƙe wani muƙami a matakin ƙasa, don haka muka ga dacewar mu kafa wannan ƙungiya don taimakon na baya mu sanya su a hanya su ma su zama ƙwararru kuma su shiga irin wannan ƙungiyoyin na ƙwararrun.”

Ya ce, ƙungiyarsu na duba matsalolin da jihohin biyu ke ciki sannan su ga rawar da za su iya takawa akai. Yana mai cewa, “Ko a lokacin zuwan korona mun shirya bita, kuma Alhamdulillahi gwamnonin jihohin suna ba mu haɗin kai.”

Ya ƙara da cewa, “Ya zuwa yanzu ba mu gamsu da irin rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa ba, domin a Kano da Jigawa muna da gidajen radiyo fiye da guda 30, amma dukkansu sun zama ‘yan ƙanana, akwai waɗanda suka zo bayansu a wasu jihohin yanzu suna da tashoshi a wasu jahohin a ƙasar gaba ɗaya wasu ma sun fita ƙasashen waje sun kafa.”

“Amma mu a Kano da Jigawar muna cin duduniyar juna, kowa ya zama ‘yar ƙaramar tasha wasu ba ma sa iya biyan albashin ma’aikata.”

Shi ma a jawabinsa, Alhaji Muhammad Ibrahim OFR MNI Makaman Rungim kuma  tsohon Janar Manaja na NTA da FRCN ya ce, wata dama suka samu don a tattauna matsaloli da kafafen yaɗa labarai ke fuskanta  ta yadda za a magance su kuma su ɗaurewa masu kuxi don su buɗe gidajen Radiyo da Talabijin don bunƙasar waɗannan jihohi namu.”

Taron ya samu halartar manya manyan  mamallaka da shugabanin kafafen yaɗa labarai kamar su Freedom Radiyo, Jalla Fm Radiyo, Libaty TV/Radiyo Tambarin Hausa TV da NTA ARTV  Sawaba FM Dandal-Kura FM da Farfoshoshi da Daktoci na Tsangayar Koyar da Aikin Jarida da Tsangayar Koyar da Kasuwanci na makarantar Dangote, da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *