Ba mu yanke shawarar barin APC ba, inji Ɗanmalikin Kabi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ƙungiyar nan mai rajin lalubo nagartattun shugabanni (Likemind Initiative For Good Governance) a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Musa Abubakar Ɗanmalikin Kabi ta ce har yanzu ba ta yanke shawarar barin Jam’iyyar APC ko kuma ta tsayawa a cikinta ba har yanzu.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa Alhaji Musa Abubakar Ɗanmalikin Kabi ne ya bayyana haka bayan kammala wani taron masu ruwa da tsaki na wannan ƙungiyar da aka gudanar a ɗakin taro da ke Unity Hall a garin Birnin Kebbi ƙarshen makon da ya gabata.

Alhaji Musa Abubakar Ɗanmalikin Kabi ya bayyana cewa tun shekarar 2015 da suka yi ruwa da tsaki suka bi dare da rana wajen kafa wannan gwamnatin bisa ga hasashen samun sauƙi wajen talaka amma abin ya faskara saboda halin ko-oho daga waɗanda ke riƙe da madafun iko musamman a jihohi da kuma waɗanda ke zagaye da shugaban ƙasa.

Ba shakka duk wanda ya san Buhari ya san mutumin kirki ne sai dai Allah ya jarrabe shi da miyagun makusanta da ba su gaya masa gaskiyar al’amari kuma ba su bari a kusance shi balle a faɗa masa.

Ya ƙara da cewa, “wannan taron an shirya shi ne domin bai wa kowa haƙƙinsa na da ɗan ƙungiya saboda a matsayin mu na shugabanni ba za mu yanke shawarar barin Jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyyar ba ba tare da bai wa kowa haƙƙinsa ba.

“Saboda haka yanzu dai mun yanke shawarar tattaunawa tsakanin shugabannin ƙungiya daga ƙananan hukumomi ashirin da ɗaya da ke Jihar Kebbi sannan za mu gaya wa duniya matsayar da muka yi,” inji shi.

Duk da ya ke dai a wata ƙwarya-ƙwaryar jin ra’ayi da waɗannan shugabannin suka yi ta nuna alƙiblar akwai yiyuwar sauya jam’iyya amma sai dai ba wanda ya ayyana inda za su dosa duk da ya ke dai a jihar Kebbi Jam’iyyar APC mai mulki sai kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP ne ke da tasiri.