Ba mu yarda a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba – APC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kwamitim yaƙin neman zaɓe na ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyya mai mulki APC, ya ce buƙatar da jam’iyyun hamayya suke gabatarwa ta soke zaɓen, ba za ta taɓa yiwuwa ba.

Kwamitin ya bayyana haka ne a matsayin martani ga taron manema labarai da manyan jam’iyyun hamayya uku, PDP da LP da kuma APC suka yi inda suka ce sai dai a soke zaɓen na ranar Asabar.

Kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen na APC Festus Keyamo, ya ce shugaban hukumar zaɓen ta INEC zai saɓa doka idan har ya soke zaɓen da tuni ya riga ya fara bayyanawa.

Keyamo ya ce, ”buƙatar ba mai yuwuwa ba ce bisa doka. Suna gabatar da buƙatar da ta saɓa doka.”

Ya ce, mafita ɗaya ce kawai ga ‘yan hamayyar a yanzu, ita ce su je kotu idan ba su amince da sakamakon zaɓen ba.