Ba na maganar yin sulhu da Ganduje – Kwankwaso

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta wasu raɗe-raɗi da ke yawo da ke bayyana cewa yana tattaunawa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje don yin sulhu.

Yayin wata hira da Channels TV da yammacin ranar Lahadi. Kwankwaso ya ce ya ji daɗin ziyarar ta’aziyyar da Ganduje ya kai masa kwanakin baya, amma bayan wannan ziyara ta gaisuwa babu wata magana da ake yi a bayan fage dangane da yin sasantawa.

Ya bayyana yadda alaƙarsa ta kasance da Gandujen a baya tun lokacin da ya yi mata mataimakin gwamnan Kano a zaɓen 1999, da kuma yadda suka ci gaba da aiki tare har zuwa 2015 lokacin da suka raba garin bayan ya zama gwamna.

An tambaye shi cewa to shin yanzu idan ka samu wata dama za ka sake bayar da sunan Ganduje kamar yadda ka yi a baya?.

Sai ya kaɗa baki ya ce ”a yanzu dai ka san ba a jam’iyya ɗaya muke ba, don haka ina ga babu ma buƙatar yin wannan tambaya, don haka ko da dama ta samu akwai mutanen da suka cancanta cikin waɗanda nake tare da su.”

Alaƙa tsakanin shugabannin biyu ta daɗe da yin tsami  tun bayan da Kwankwaso ya miƙa wa Ganduje ragamar mulkin Kano a 2015 bayan sun shafe shekara takwas a matsayin gwamna da mataimaki. har ta kai ga yanzu Kwankwaso ya koma jam’iyyar adawa ta PDP.

Sai dai Gwamna Ganduje na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida a jam’iyyarsu ta APC tsakaninsa da tawagar tsohon gwamna kuma sanata a yanzu, Malam Ibrahim Shekarau.

Rikicin siyasar Kano dai na ci gaba da kankama musamman a jam’iyyar APC mai mulki, inda tsagin tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau ke rikici da ɓangaren Ganduje kan shugabancin jam’iyya.

Haka ma a PDP har yanzu tana ƙasa tana dabo tsakanin ɓangaren Kwankwaso da na tsohon ministan harkokin wajen Nijeriya Ambasada Aminu Wali, wanda shi ma vangarensa ke adawa da jagorancin Kwankwaso.