Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Tsohon Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Alhaji Muhammad Bello ɗantani (Magajin Rafin Kabi) ya ƙaryata maganganun da suka karaɗe kafofin sada zumunta na zamani na cewa zai tsaya takarar kujerar ɗan majalisar dattawa a zaɓen shekarar 2027.
Wannan bayanin ya fito ne daga bakin mai magana da yawunsa Alhaji Sama’ila Tafarki (Maina) lokacin da ya ke zantawa da wakilinmu a garin Argungu ranar Larabar da ta gabata.
Alhaji Sama’ila Tafarki ya ce maganar da ke yawo na cewa tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Bello ɗantani Magajin Rafin Kabi zai fito takarar muƙamin Sanata don wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa ba gaskiya ba ne, wannan magana ce da ba ta da asali illa dai waɗansu mutane ‘yan tada zaune tsaye ne suka ƙirƙiro ta kuma suka bazawa duniya.
Ya ƙara da cewa akwai yiyuwar ganin yadda ya yi wani zagaye ne a wannan yankin tare da raba kuɗaɗe ga ‘yan siyasa musamman magoya bayansa ne saboda hidimar iyali a wannan watan mai alfarma na azumi shi ne ya baiwa waɗansu da ke jiran wani dalili ƙiris su yi amfani da wannan damar su yaɗa ƙanzon kurege tsakanin al’umma, amma dai maganar gaskiya ba maganar takarar kowace irin kujera.
Kamar yadda mafi yawan mutanen jihar Kebbi suka sani a duk irin wannan lokacin na watan azumi ko lokacin Sallar layya ya kan yi rabon kuɗi ga ‘yan siyasa musamman magoya bayansa domin hidimar azumi ko kuma sayen dabbobin layya.