Ba ni da allon kwaikwayo a harkar rubutun adabi – Sadiya Abdulrazaƙ

“Rubutu ba ya hana ni karatun littattafai”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Tauraruwar adabin mu ta wannan mako ba wata ba ce illa Malama Sadiya Abdulrazaƙ daga Jihar Jigawa, wacce ta kasance daga irin marubutan nan masu inganta saƙonnin da suke isarwa ga al’umma da kuma kyautata ƙa’idojin rubutu. Duk yadda ka kai ga gudun karatun onlayin idan ka ci karo da littafin Sadiya, sai ka tsaya ka duba. Tana da wani salo mai ƙayatarwa da riƙe mai karatu, wanda ya sa ta fita daban da wasu da dama. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya nemi sanin ko abin da ke zaburar da ita ga yin rubuce-rubuce. Za ku ji amsar da ta ba shi idan kun nutsa cikin karatun tattaunawar da suka yi. 

MANHAJA: Mu fara da sanin ke wacece? Kuma me ki ke yi a rayuwa?

SADIYA: Sunana Sadiya Abdulrazaƙ Lawan. Ni asalina ‘yar Jihar Kano ce daga ƙaramar Hukumar Nasarawa, amma yanzu ina a zaman aure a ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa. Ni marubuciya ce, kuma ‘yar kasuwa. Ina da iyali da yara uku. 

Ko za mu san tarihin rayuwarki?

Ni haifaffiyar Jihar Kano ce, mahaifina ɗan asalin Jihar Katsina ne, mahaifiyata kuma daga Jihar Nasarawa. An haife ni a shekarar 1999, cikin Unguwar Brigade da ke ƙaramar Hukumar Nasarawa. Na yi makarantar firamare a nan cikin unguwarmu, a Gwagwarwa Special Primary School, sannan na yi makarantar sakandiren Gwamnati ta ‘Yammata a nan G.G.S.A.I.S.S Gwagwarwa. Bayan na kammala daga nan ban samu na cigaba da karatu ba, sai aka yi mini aure a shekarar 2016. Yanzu haka ina da yarana uku. 

Wanne irin yanayin iyali ki ka fito? Kuma wacce tarbiyya ki ka samu a lokacin tasowarki?

Na fito ne daga cikin iyali masu takatsantsan da kula da tarbiyyar yara sosai, kuma Alhamdulillah na samu tarbiyya daidai gwargwado. Mun taso cikin rayuwa tsakanin gida da makaranta, babu wasu sabgogi, sai karatu da neman ilimi.

Mene ne ya fara jan hankalinki zuwa karatun littattafan Hausa?

Zaman kaɗaici ne ya fara jan hankalina har na yi sha’awar fara karatun littattafan Hausa, wanda a baya ban saba da yi ba. 

Tun yaushe ki ka fara tunanin ke ma ki rubuta naki littafin?

Lokacin da karatun littattafan da nake yi ya fara zurfi sosai, a sannan ne na fara tunanin ni ma fa zan iya rubuta nawa littafin. Na fara wannan tunanin ne kuwa a shekarar 2019.

Shin za ki iya tuna labarin da ki ka rubuta na farko, akan wanne jigon ki ka yi?

Labarin da na fara ɗora alƙalamina a kansa shi ne, ‘Burina Ya Ja Min’, wanda na gina shi akan jigon kwaɗayi.

Wane ne ya fara koya miki ƙa’idojin rubutu da dabarun rubutun labari, har ki ka kai matakin da ki ke yanzu?

Ba zan taɓa mantawa ba, Shugabar ƙungiyar mu ta First Class Writers Association, Aisha Adam Hussaini, Gwarzuwar Hikayata ta 2023, ita ce wacce ta fara koya min sanin ƙa’idojin rubutu, daga nan ta saka ni a ƙungiyarta, aka cigaba da nuna min abubuwa kan dabarun tsara rubutun Hausa, ta sanadin ta ne na san ƙa’idojin rubutu.

Wanne littafin ne ya fara fitar da sunanki a duniyar marubuta?

Littafina mai suna ‘Matar Shige Ba Ta Daraja’, shi ne ya fara fito da sunana a duniyar rubutu, har mutane da dama suka fara sanina, da bibiyar littattafaina.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa? Kawo mana sunayen su.

Alhamdulillahi. Kawo yanzu dai na rubuta littattafai guda 15, a cikinsu akwai 

‘Matar Shige’, ‘Alhakin So’, ‘Mataccen Buri’, ‘Zai Gyaru’, ‘Iya Ruwa’, ‘Wani Auren’, ‘Da Walakin’, ‘Mukullin Nadama’, ‘Kausar’, ‘Mishkila’, ‘Gajen Haƙuri’, ‘Likitana’, ‘Wutar ƙaiƙayi’, ‘Zuciyar Mace’, sai kuma, ‘Ku Yi Mana Adalci’. 

Ko za ki iya mana bitar fitattu uku daga cikin littattafan da ki ka fitar, da darussan da suke koyarwa?

Da farko zan ɗauki labarin ‘Wani Auren’, wanda jigonsa ya danganci zamantakewar aure. Daga cikin darussan labarin akwai matsalar da mace take jefa namiji ta hanyar hana shi haƙƙinsa na auratayya, da kuma matsalar da namiji yake saka mace ta hanyar yawace-yawacen garuruwa da sunan kasuwanci, a yi nesa da mace. Sannan akwai ƙalubalen da mata masu fita aikin gwamnati ke fuskanta, yayin da suke barin mazajensu da ‘ya’yansu a gida.

Sai littafi na biyu, mai suna ‘Alhakin So’, shi kuma jigon sa shi ne yaudara. A cikin labarin na nuna irin matsalar da ke tattare da zurfafawa a soyayya, musamman daga wajen mace, wacce ta kasance mai rauni, maza da dama sukan yi amfani da wannan damar wajen cutar da ita.

Littafi na uku kuma, ‘Iya Ruwa Fid-da Kai’, labari ne da na gina jigon sa akan kishi. Na nuna yadda zaman kishi yake, ba dole sai da boka ko malam mace za ta yi fice cikin kishiyoyinta ba. Sannan na fito da matsalolin da rashin adalci daga wajen miji yake janyowa.

Kin taɓa fuskantar wani ƙalubale ta dalilin rubutu, daga gida ko daga masu karatu?

Zuwa yanzu dai gaskiya ban taɓa fuskantar kowacce irin matsala ko ƙalubale ta sanadin rubutu ba. Alhamdulillah. 

Yaya alaƙar ki take da masu bibiyar littattafanki? Ta yaya ki ke fahimtar ra’ayinsu akan labaranki?

Alaƙata da masu bibiyar rubutuna, alaƙa ce mai kyau, da yawansu mun zama ƙawaye, wasu kamar ma ‘yan’uwa. Babu komai tsakaninmu sai aminci da girmama juna. Ina fahimtar ra’ayinsu ne ta hanyar yawan sharhinsu a kan labari, da kuma yabawarsu.

Mene ne yake zaburar da ke wajen fitar da labarinki ga masu karatu? Kuma me yake kashe miki gwiwa?

Idan na ji masu bibiyata suna faɗin, “Sadiya, don Allah yaushe za ki fara yi mana sabon labari?” “Labarinki kaza da na karanta ya yi ma’ana sosai.” Waɗannan kalaman ne suke zaburar da ni na ji ina son rubuta sabon labari. Babu wani abu da yake kashe min gwiwa wajen yin rubutu. In dai na samu isasshiyar dama da kuma ra’ayi to, kawai zan yi shi, ko da babu ma su sharhi.

A wacce ƙungiyar marubuta ki ke? Kuma wacce gudunmawa take ba ki wajen inganta rubutunki?

Ina cikin ƙungiyar First Class Writers Association ne tun farkon fara rubutuna har yanzu. ƙungiyata abar alfaharina ce, domin komai na zama a harkar rubutu ta sanadinta ne. Haƙiƙa ta yi min matuƙar ƙoƙari wajen inganta rubutuna, da koyon dabarun rubutu.

Wanne alheri ne ya taɓa samunki a dalilin rubutu wanda ba za ki manta ba?

Akwai wata mata da ta karanta labarina ‘Wani Auren’, sanadin haka ta yi mini addu’ar da na ji daɗinta sosai, tare da kyauta mai nauyi. Ba zan manta da wannan ba.

Kamar yadda muka sani adabi ya kasu kashi-kashi, tsakanin rubutun zube, rubutun waƙoƙi, da rubutun fim ko wasan kwaikwayo, wanne ki ka fi sha’awar yi?

Rubutun zube shi kaɗai nake sha’awar yi.

Kin taɓa shiga wata babbar gasar rubutun gajeren labari? 

Babbar gasa ɗaya zan ce na taɓa shiga, ita ce ta Hikayata ta BBC Hausa, kuma har yanzu Allah bai kawo nasarar ba tukunna.

Bayan kasancewarki marubuciya, shin kina iya karanta littattafan wasu marubutan? Wanne littafi ne yanzu ki ke karantawa?

Haƙiƙa rubutu ba ya hana ni karatun littattafai. Ba na taɓa zama na yi kwana uku ban yi karatu ba. A yanzu haka ina karanta labarin ‘Rana ɗaya’ ne na Halima K/ Mashi.

Waɗanne marubuta ne suke zaman iyayen gidanki ko allon kwaikwayonki?

Ba ni da wani tsayayyen ubangida a harkar rubutu, sai dai nakan bibiyi duk wani darasin da na san zan samu ilimin inganta rubutuna da shi. Haka shi ma allon kwaikwayo babu.

Mene ne yake burge ki da harkar rubutu da rayuwar marubuta?

Abin da yake burge ni a harkar rubutu shi ne yadda nake tura saƙon da dubban mutane za su karanta, ina daga kwance a ɗakina. Zaman marubuta a inuwa ɗaya wato ƙarƙashin guruf da kuma haɗin kansu yana matuƙar burge ni shi ma.

Kina da wata shawara ga ‘yan uwanki marubuta?

Shawarata ga marubuta ita ce su ƙara zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, ta hanyar haɗa kai. Manyan cikinsu, su riƙa tallafawa ƙananan kamar yadda su ma aka tallafe su, sannan su tsarkake alƙalumansu, su gujewa rubuta shirmen da zai iya yaga rigar mutuncinsu da ma ahalinsu bakiɗaya.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Idan da akwai karin maganar da take tasiri a rayuwata ba zai wuce wannan ba, Ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne! 

Mun gode.