Ba ni da masaniyar kayar da APC a zaɓen Osun – Shugaban APC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Lahadi ya yi ikirarin rashin sanin nasarar ɗan takarar jam’iyyar PDP kuma zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke.

Adeleke ya doke ɗan takarar jam’iyyar APC, Gboyega Oyetola a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ƙarshen mako.

Rahotanni sun nuna cewa, tun daga lokacin ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya ɗan takarar PDP murna. Sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa ta yi shiru kan sakamakon zaɓen.

Da ya ke magana a cikin shirin da ake sa ido a gidan talabijin na Arise, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya ce, har yanzu ba a sanar da shi sakamakon zaɓen ranar Asabar a jihar Kudu maso Yamma ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *