Ba ni da zaɓin wani wanda nake so ya zama Kakaki ko Shugaban Majalisa – Tinubu

Daga AMINA YUSUF ALI

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa, sam shi ba shi da wani wanda ya fi so ya zama shugaban majalisun dokoki guda biyu da ake sa ran za su kafa majalisa a karo na 10 a Nijeriya.

Tinubu, wanda zaɓaɓɓen Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da sababbin zaɓaɓɓun ‘yan majalisun.

Majiyarmu ta bayyana cewa, a yanzu dai, Tinubu ya ce har yanzu ba shi da wani wanda ya zaɓa da yake son ya shugabanci majalisun guda biyu, wato shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai.

Amma a cewar majiyar tamu, za a ci gaba da tuntuɓar juna domin ganin jamiyyarsu ta samu nasarar lashe zaɓe a zaɓe mai zuwa na na gwamnoni da majalisun dokkokon jihohi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *