Ba siyasar jahilci muke yi ba – Ogan Ɓoye

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Hon. Yusuf Imam, wanda aka fi sani da Ogan Ɓoye, ya bayyana cewa su ba sa siyasar jahilci, kuma bai yin siyasar gaba ko nunin yatsa, a cewarsa yana siyasa ne ta mutunci da mutunta juna.

Ogan Ɓoye wanda jigo ne a tafiyar NNPP ta Kwankwasiyya, kana makusanci ga Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, rahotanni sun bayyana cewa magoya bayansa sun nuna fushinsu da cire wasu hotuna, kan rashin bashi takarar Sanatan Kano ta Tsakiya wanda Sanata Rufai Sani Hanga ya samu takarar bayan ficewar Malam Ibrahim Shekarau, Sardaunan Kano daga Jam’iyyar NNPP.

Ogan Ɓoye ya ce shi mabiyin Ɗariƙar Tijjaniya ne kuma muridi ne na Marigayi Aliyu Shehu Harazimi, wanda, “tauhidi ne ke a matsayin jagora na rayuwa na cewa samu da rashi duk daga Allah maɗaukakin Sarki ya ke, wannan ya nuna cewa mu ba siyasar jahilci muke ba duk abin da Allah ya ƙaddara zai bani to zai bani babu wata makawa ko wani da zai iya hanani, don haka wanda aka ce sun yi hayaniya ko hatsaniya da suna na ba ni da wannan labarin domin ni ma bana Kano ko awa 24 ban yi ba Kano.”

Hon. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya bayyana haka ne ga ‘yan jarida a safiyar ranar Lahadi da ta gabata a gidansa da ke birnin Kano.

Har ila yau ya ce a matsayin sa na wanda ya ke tare da matasa shekara da shekaru ba siyasa ce kawai ta haɗa shi da matasa ba ko da siyasa ko ba siyasa su na tare da matasa sakamakon harkokin sana’ar su da kasuwancinsu da kyakyawar mu’amala, taimakonsu ta zamatakewar rayuwa ta yau da kullum, “wanda kuma wannan abin godiya ne ga Allah Maɗaukakin Sarki da ake zaune da jama’a lafiya.”

A ƙarshe Ogan Ɓoye, ya yi kyakyawar fatan alkairi da nasara ga ɗaukacin mabiya Kwankwasiyya da sauran al’ummar Nijeriya, musamman masu riqon amana, gaskiya da jajircewa da kuma yin addu’a kan Allah ya ƙarawa Kano zaman lafiya da tarin arziki, tsaro, da sauransu, kana Allah Ya ba Nijeriya shugabanni nagari a zaɓen gama-gari na 2023 idan Allah ya kaimu lafiya.