Ba wanda za a buɗe wa layin waya har sai ya yi rajistar NIN, cewar hukuma

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar da take kula da harkokin sadarwa a Nijeriya (NCC)  ta bayyana cewa, daga cikin lauyukan da hukumar ta rufe, babu wanda za a buɗe wa layin har sai ta/ya yi wa layinsa rajistar lambar shaidar ɗan ƙasa wato, NIN.

Wannan bayani yana ƙunshe ne a cikin wani jawabi da hukumar NCC ɗin ta wallafa wanda yake ɗauke da sa hannun Daraktan harkokin jama’a na hukumar, Dakta Ikechukwu Adinde.

Adinde ya ƙara da cewa, wannan jawabi yana da matuƙar muhimmanci ga al’umma duba da yadda wasu suke watsa adireshin yanar gizo na bogi a yanar gizo a matsayin inda za a shiga don buɗe layukan da aka rufe. 

A cewar sa, waɗancan adireshi da ake ta yaɗawa wata hanya ce ta dulmiyarwa da cutar al’umma ta hanyar ba su bayanan ƙarya game da rajistar NIN da kuma yadda za a buɗe layukan wayoyin da aka rufe. 

Ya ƙara da cewa, sam waɗannan bayanai ba daga NCC suke ba. Domin a cewar sa, babu layin da za a iya buɗewa ba tare da yi wa layin rajista da lambar NIN ɗin mai amfani da layin ba. Waɗanan bayanai a cewar sa an yi su ne don a cutar da masu tsautsayi daga cikin al’umma.

Adinde ya ce: “Hukumar sadarwa ta Nijeriya (NCC) a hukumance tana sanar da al’umma masu amfani da layukan sadarwa  (SIM) da aka dakatar da layukansu daga kiran waya cewa, kamfanonin sadarwar ba za su tava buɗe musu layukan nasu ba har sai sun yi wa layukansu rajistar lambar shaidar ɗan ƙasa, NIN”.

Domin a cewar sa, mutane suna yaɗa bayanan ƙarya a shafukan ƙarya na yanar gizo har ma sukan ɗora logon hukumar ta NCC don kawai su yaudari mutane. Wannan ya sa hukumar ta ga ya zama dole ta fito ta yi wa al’umma wannan bayani don kawar musu da shakku don gudun kada su afka tarkon ɓata-gari. 

Don haka a cewar sa, al’umma kawai su je su yi wa layukansu rajistar NIN don babu wata hanya ta buɗe musu layi sai sun yi hakan. Kuma hukumar  NCC a matsayinta na mai kula da dukkan kafofin sadarwa a Nijeriya ta sanya wannan dokar ne don bin umarnin gwamnatin Tarayya na tabbbatar da kowanne layin waya an yi masa rajistar lambar NIN.

Ya ƙara jaddada cewa, hukumar ba za ta taɓa yarda ta take dokar gwamnatin tarayya ta buɗe layukan waɗanda ba su cika sharuɗɗan da ta nema ba. Don haka, yake kira da al’ummma da su bi hanyoyin da suka dace. Kuma a cewar sa, gwamnatin ta yi wannan dokar domin ƙara inganta tsaro a ƙasar nan. 

Daga ƙarshe, hukumar NCC ta yi jan hankali ga mutane da su kiyayi bayanan da ake ta watsawa a yanar gizo musamman shafukan Tiwita da cewa hukumar NCC tana neman ma’aikata. Wannan bayani a cewar hukumar ba shi da makama balle tushe.