Ba za a biya diyya ba don kuɓutar da ɗaliban Kagara, Minista Lai

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnatin Tarayya ta ce babu wata diyya da za ta biya domin kuɓutar da ɗalibai da malaman sakandaren Kagara da aka yi garkuwa da su.

Kazali, ta ce ba ta biya diyya ba wajen kuɓutar da ɗaliban Ƙanƙar da aka sace a jihar Katsina da kuma waɗanda aka kwashe a Dapchi, jihar Yobe.

Ministan Larabarai da Raya Al’adu, Mr Lai Mohammed ne ya yi wannan bayani yayin tattaunawar da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels a safiyar Asabar, inda ya yi magana a kan ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen daƙile matsalar sace-sacen mutane ta ke faruwa a ƙasa.

A cewar Lai, “Duka labarun da ake yaɗawa kan an biya diyya, makirci ne kawai.”

Ministan ya yi waɗannan bayanan ne ‘yan kwanaki da sace ɗalibai da malamai a Kwalejin Kimiyya da ke Kagara a Jihar Neja.

Da yake amsa tambaya game da batun ɗaliban Kagara da aka sace, Lai ya ce gwamnati ba ta zauna ba, tana nan tana yin dukkan mai yiwu domin magance matsalar.