Ba za a rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa ba – Ezeife

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon gwamnan jihar Anambara, Chukwuemeka Ezeife, ya ce, ba za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya ba.

Ezeife ya bayyana haka ne a yayin da ya ke zargin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC da yin maguɗin zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa da na ’yan majalisun tarayya inda jam’iyyarAPC da ɗan takararta Bola Ahmed Tinubu suka marawa baya.

Tsohon shugaban na Anambra ya ce, a fili yake cewa Peter Obi na jam’iyyar LP ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a faɗin ƙasar.

Shugaban Hukumar INEC, Mahmood Yakubu, da sanyin safiyar Larabar nan, ya ayyana ɗan takarar shugaban qasa na jam’iyyar APC, Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Yakubu ya ce, Tinubu ya samu quri’u 8,794,726 inda ya kayar da abokan hamayyarsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar Labour, LP wanda ya samu 6,984, 520 da 6,101,533 bi da bi.

Sai dai Ezeife ya shaidawa gidan talabijin na Arise Morning Show cewa zaɓen shugaban ƙasan ya bayyana wa ‘yan Nijeriya abubuwa da dama.

Ya ce, “Ina godiya ga ɗaukacin ƙasashen waje da suka yi tsokaci tare da yin Allah wadai da sahihancin zacen kuma ina godiya ga ɗaukacin ’yan Nijeriya kan yadda suka yi da jam’iyyar LP.