Majalisar Dattawa ta Nijeriya ta hannun kwamitin Kuɗi ƙarƙashin jagorancin Sanata Sani Musa, ta yi gargadi ga hukumomin gwamnatin tarayya da ke ƙin bayar da rahotannin yadda suka kashe kuɗaɗen kasafin kudinsu na shekarar 2024. Sanatan ya bayyana haka a wani bincike na musamman a ranar Litinin cewa majalisar za ta dakatar da ware kuɗaɗe ga duk wata hukuma da ba ta bi umarnin majalisar ba na bayar da bayanan kuɗaɗe.
A yayin ganawar da Akanta Janar na Tarayya, Miss Oluwatoyin Madein, kwamitin ya nuna rashin jin daɗin sa da tsarin biyan albashi na bai ɗaya wato IPPIS da ofishin Akanta Janar ke sarrafawa, inda ya bayyana damuwa game da jinkirin sakin kuɗaɗen kasafin kuɗi da kuma amfani da su.
Rahotanni sun nuna cewa akwai rashin tsari a cikin bayanan kuɗin da wasu hukumomi suka gabatar, wanda ya sa aka yi duba kan kuɗaɗen da ake samu ta hanyoyin gwamnati, bin diddigin kuɗaɗen da kuma yanayin yadda ake gudanar da kuɗi a ƙasar gaba ɗaya.
A cikin jawabinta, Mis Madein ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu jimlar kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 2.7 daga kuɗaɗen da hukumomin gwamnati suka samar da kansu (Independent Revenue), sai kuma Naira tiriliyan 2.3 daga rarar da hukumomi suka samu (Operating Surplus), wanda ya ƙunshi kuɗaɗen shiga na cikin gida da ma’aikatu (IGR). Sai dai kwamitin ya caccaki rahoton saboda rashin cikakkiyar bayani, kasancewar ya ta’allaƙa ne kawai kan bayanan Ofishin Akanta Janar ba tare da haɗa sauran hukumomin gwamnati ba.
Sanata Musa ya bayyana cewa, don samun gaskiya da daidaito, wajibi ne a gayyaci dukkan hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Hukumar Rarraba Kuɗaɗen Gwamnati da Tattalin Arziki (RMAFC), Hukumar NEITI, da kuma Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), domin yin cikakken nazari kan rashin daidaito a rahotanninsu.
Majalisar ta kuma nuna damuwa kan ƙarancin kuɗaɗen haraji, wanda ya kai Naira miliyan 30.3 daga shekarar 2020 zuwa 2024, idan aka kwatanta da Naira miliyan 301.49 da aka samu ta sauran hanyoyin samun kuɗin shiga.
Mai rikon muƙamin akanta janar ta bayyana cewa an ɓullo da tsarin biyan albashi na bai ɗaya wato IPPIS ne don rage almubazzaranci da kuma daƙile duk wani abin da zai sa a mayar da kuɗaɗen da ba a kashe su ba a duk shekara.
Duk da haka, kwamitin ya ba ta wa’adin har zuwa ranar Laraba don gabatar da ƙarin rahotanni, yayin da aka tsara ci gaba da zaman tattaunawa a wannan rana.
Haka kuma, majalisar ta nuna aniyar gayyatar sauran hukumomi don tabbatar da ganin an warware duk wata matsala da ke akwai a cikin bayanan kuɗaɗen da suka gabatar.