Ba za mu ƙara zaman tattaunawa da gwamnatin Buhari ba – ASUU

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Biyo bayan mayar da yajin aikin da ta ke yi zuwa na sai abin da hali ya yi, Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta ce, akwai yiwuwar ba za ta kara zaman tattaunawa da gwamnati ba har wa’adin mulkin Shugaban Buhari ya ƙare.

Wani mamba daga kwamitin zartarwar ƙungiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, yayin da zu su ci gaba da gudanar da yajin aikin sai baba-ta-ganin, sun rufe tattaunawa da gwamnati.

Haka kuma ya ce, gabanin fara tattaunawa a taron da ƙungiyar ta gudanar da ’ya’yanta, an samu hayaniya, musamman kan batun da shugaban ƙungiyar Emmanuel Osodeke ya yi da ke nuna raini ga jami’un.

“Malamai da yawa daga jami’o’in ABU da BUK da FUD da na Kudancin Nijeriya na ganin tattaunawar da ake yi da gwamnatin ba ta da wata fa’ida, don haka a dakatar har sai gwamnatin ta sauka a 2023.

“Ba wai ba mu da tausayi ba ne, don mu ma ya shafe mu, ko ni ina da ’ya’ya a jami’o’in nan, kuma watansu shida a gida.

“Sannan tsawon watanni shidan nan ba na karɓar albashi, amma hakan bai hana ni yin abin da ya dace ba domin ceto su daga lalacewa”, inji shi.

A wani labarin kuma, Shugaban Ƙungiyar Dalibai na Ƙasa (NAN) Asefon Sunday, ya ce, ƙarin wa’adin yajin aikin ASUU saboda ƙin biyansu albashin wata shida son zuciya ne mararatan suka nuna.

“Kashi 85 na buƙatun ASUU an samu matsaya a kansu, amma saboda son zuciya sun ki janye yajin aiki.

“Suna kuma yaudarar mutane da batun gyaran jami’o’i, amma yaƙi kan walwalarsu ya fi yawa a batun yaji aikin,” inji Shugaban na NANS.

Shi ma dai Kakakin Ma’aikatar Ilimi ta Ƙasa, Bem Ben Goong, ya ce, ba hurumin ASUU ba ne dagewa sai gwamnati ta sauya tsare-tsarenta.

Ya ce, aikin ASUU a dokance kamar sauran ƙungiyoyi shi ne ƙoƙarin samarwa ’ya’yanta walwala, sai dai kaso 95 na buƙatunta na 2009, ba kan haka ba ne.

Haka kuma ya yi Allah wadai da batun ASUU na cewa su ne sanadiyyar kawo ci gaban jami’o’in kawo wannan lokacin.