Ba za mu bari a sake samun aukuwar yaƙi a ƙasa ba – Dattawan Arewa

Daga BASHIR ISAH

Sakamakon tashin-tashinar da ke aukuwa a yankin Kudu-maso-gabas, Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta yi kira ga shugabannin ƙabilar Igbo da su ja kunnen masu tada zaune tsaya a yankin da su maida wuƙaƙensu cikin kube domin hana sake aukuwar yaƙi a ƙasa.

Ƙungiyar ta yi wannan furuci ne sa’ilin da take yi wa manema labarai bayani a Litinin da ta gabata a Abuja jim kaɗan bayan kammala wani taronta.

NEF ta ce biris da shugabannin Igbon suka yi ba su ce komai ba hakan ya nuna ba su damu da kisan da ake yi wa ‘yan Arewa a yankin ba.

A cewar mai magana da yawun ƙungiyar, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, dattawan Arewa sun yanke shawarar ba za su bari a sake samun aukuwar yaƙi a ƙasa ba, tare da cewa shurun da shugabannin Igbon suka yi hakan na nufin suna goyon bayan masu tada ƙayar baya na yankin nasu ne.

Dattawan Arewa sun ce shugabannin siyasa na yankin Kudu-maso-gabas, sun yi mubaya’a ga IPOB da shirin banga na ESN a yankin.

Baba-Ahmed ya nuna takaicinsa kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da yi wa rayuwar jama’a barazana a sassan ƙasa da kuma yadda ‘yan ta’adda ke ta samun tagomashi a yankin na Kudu-masu-gabas da wasu sassan ƙasa.

Da wannan NEF ta yi kira ga gwamnatin ƙasa da a hanzarta cafkewa da hukunta duk waɗanda ke da hannu wajen tada ƙayar baya don tabbatar da zaman lafiya.

A hannu guda, dattawan Arewan sun yi kira ga Majalisar Ƙasa da ta ɓullo da sabbin hanyoyin da za ta yi amfani da su wajen tattara ra’ayoyin da za su taimaka wajen gyara wa sha’anin shugabancin ƙasa zama kafin nan da zaɓuɓɓukan 2023.

Sun ce, “A shirye Arewa take ta shiga tattauna batutuwan da ke da alaƙa da gyaran kundin tsarin mulki da sake fasalin ƙasa tare da jagororin ƙasa da kuma ƙungiyoyin da suke son ci gaban Nijeriya.”